Chelsea ba ta sa Sterling cikin Europa Conference League ba

Asalin hoton, Getty Images
Chelsea ba ta sa sunan Raheem Sterling ba, cikin waɗanda za su buga mata karawar cike gurbin shiga Europa Conference League da za ta kara da Servette.
Wasa na biyu kenan da aka ajiye mai shekara 29, bayan da bai buga wa Chelsea karawar da Manchester City ta yi nasara 2-0 a Premier League ranar Lahadi.
Haka kuma Chelsea ba ta sa sunan Ben Chilwell da Wesley Fofana da kuma Tosin Adarabioyo ba, cikin waɗanda ta aike wa da hukumar ƙwallon kafa ta Turai, Uefa.
Ranar Alhamis, Chelsea za ta buga wasan a Stamford Bridge, wadda take fatan samun gurbin shiga Europa Conference League ta bana.
Ranar Lahadi wakilan Sterling suka fitar da sanarwar neman makomar ɗan wasan, bayan da ba a saka sunansa cikin waɗanda za su fuskanci City ba a Premier.
Chelsea ta kashe £185m wajen sayen ƴan wasa 11 tun kan fara kakar bana, kenan koci, Enzo Maresca yana da manyan ƴan ƙwallo sama da 40 a kasa.
Haka kuma Chelsea ta amince ta sake ɗaukar Joao Felix daga Atletico Madrid, ita kuma za ta bayar da Conor Gallagher.
Chelsea, wadda za ta karbi bakuncin wasan farko ranar Alhamis, za ta je Switzerland fafatawa ta biyu ranar 29 ga watan Agusta.
Sai dai idan Chelsea ta samu gurbin shiga gasar zakarun Turan, watakila ta saka sunan Sterling cikin ƴan wasan da za ta yi amfani da su a kakar bana.
Sterling, wanda ya koma Chelsea daga Manchester City kan £50m a Yulin 2022, ya buga wa ƙungiyar Stamford Bridge karawa 81.










