Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Al-Nassar na zawarcin Caicedo, Rashford na fatan komawa babbar ƙungiya
Kulub din Al-Nassr na Pro League a Saudiyya na son dauko dan wasan Chelsea , na tsakiyar Ecuador Moises Caicedo, 23, wanda ake sa ran darajar shi za ta kai fam miliyan 100. (Telegraph)
Juventus na zawarcin dan wasan tsakiya na Italiya mai taka leda a Newcastle Sandro Tonali mai shekara 22, da zarar an bude kasuwar ciniki ƴan wasa. (Gazzetta dello Sport)
RB Leipzig za ta ware fam miliyan 86, domin sayo dan wasan Slovenia, Benjamin Sesko, mai shekara 21, wanda kungiyar Manchester United, da Chelsea da Arsenal ke zawarcinsa. (Bild - in German)
Tottenham za ta zage damtse a yunƙurinta na ci gaba da riƙe ɗan wasan baya na Italiya, Destiny Udogie, mai shekara 22, a bazara mai zuwa, ko da ya ke ƙungiyoyi da dama ciki har da Manchester City na son ɗan wasan. (Florian Plettenberg)
Sporting za ta sai da mai tsaron gida na Portugal, Goncalo Inacio dan shekara 23, wanda Manchester United ke cikin masu zawarcinsa. (A Bola - in Portuguese)
Benfica na nazari kan ɗan wasan gaba na Portugal mai taka leda a Chelsea, Joao Felix mai shekara 25, da ke zaman aro a AC Milan. (Record )
Juventus nazari kan karawa mai tsaron gida na Portugal Renato Veiga mai shekara 21 lokaci, a zaman aron da ya ke yi a Chelsea har kaka mai zuwa, ko dai a wani zaman aron ko ta sai da shi kan farashin fam miliyan 48. (Tuttosport )
Chicago Fire ta fara tuntuba kan ɗauko ɗan wasan tsakiya na Belgium mai taka leda a Manchester City, Kevin de Bruyne, 33, wanda kwantiraginsa zai ƙare a ƙarshen kakar nan. (Fabrizio Romano)
Marcus Rashford, mai shekara 27, na fatan tashen da ya ke yi a yanzu zai ja hankalin manyan ƙungiyoyin Turai. (Talksport)
Manchester United ta fara rubuta jerin waɗanda za su maye gurbin Rashford, duk da babu tabbacin Aston Villa za ta ɗauki ɗan wasan kan kuɗi fam miliyan 40. (Sky Sports)