Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Super Eagles za ta buga daf da karshe na 16 a Afcon 2023
Najeriya za ta buga zagayen daf da karshe karo na 16 a gasar kofin Afirka da Ivory Coast ke karbar bakunci da ake kira Afcon 2023.
Hakan ya sa ta yi kan-kan-kan da Masar a jerin kasashen da suka kai zagayen daf da karshe da yawa a gasa hudu baya a wasannin.
Super Eagles ta samu matakin ne, bayan da ta ci Angola 1-0 ta hannun Ademola Lookman ranar Juma'a 2 ga wwatan Fabrairu.
Najeriya wadda ke buga Afcon karo na 20, za ta kara a zangon daf da karshe sau 16, iri daya da bajintar Masar, wadda ta fafatawa a gasar karo 26.
Tawagar Ghana ta halarci Afcon a Ivory Coast gasa ta 24 da ta kara a wasannin, wadda ta kai zagayen daf da karshe har sau 14 da daukar kofi hudu.
Ƙasar Kamaru da Ivory Coast sun samu buga gurbin daf da karshe a babbar gasar tamaula ta Afirka sau 10 kowacce.
Koda yake sau uku Najeriya ta dauki Afcon, Masar ce kan gaba a yawan lashe kofin mai bakwai jimilla da Kamaru mai biyar.
Wasannin daf da karshe a Afcon 2023
Ranar Laraba 7 ga watan Fabrairu
- Najeriya da South Afirka
- Jamhuriyar Dimuƙuraɗiyyar Congo da Ivory Coast.