Ten Hag ya dawo da Rashford tawagar United

Asalin hoton, Getty Images
Marcus Rashford ya koma tawagar Manchester United a gasar cin kofin Zakarun Turai da za su fafata da FC Copenhagen, yayin da kociyar Erik ten Hag ya ce dan wasan ya “dage” a kulob din.
Dan wasan, mai shekaru 26, wanda ke fafutika a kakar wasa ta bana, bai buga wasan da suka doke Fulham da ci 1-0 ba bayan ƙaramin rauni da samu yayin atisaye.
Sai dai yana cikin tawagar 'yan wasan da za su fafata a wasan na ranar Laraba, inda yake neman inganta ƙoƙarinsa bayan ƙwallo ɗaya da ya ci a wasa 14 da ya buga a yanzu.
Ten Hag ya ce "yana ƙoƙari a atisaye don ya sami dawowa cikin tawagar," in ji Ten Hag.
"Marcus ya jajirce sosai a Manchester United."
Rashford shi ne ya fi zura ƙwallo a United a 2022-23 inda ya ci kwallo 30 a duka gasanni, amma sau daya kawai ya ci a kakar wasa ta bana - a lokacin da United ta sha kashi da ci 3-1 a hannun Arsenal a watan Satumba.








