Ta yaya hukumar leƙen asiri ta Ukraine ta iya kashe janar ɗin Rasha a Moscow?

    • Marubuci, Zhanna Bezpiatchuk, Ilya Barabanov, Tom Santorelli
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Majiyar BBC a hukumar tsaro da tattara bayanan sirri ta Ukraine ta tabbatar cewa jami'anta na kai hari kan sojojin Rasha da kuma manyan jam'iai da ke da hannu a yaƙin ''duk inda abokan gaban Ukraine suke''.

Ciki har da yankunan da aka mamaye a Ukraine, da ita kanta Rasha da kuma ƙasashen waje.

Kisan laftanar Janar Igor Kirillov da ake tunanin an yi shi ne da wani abin fashewa da aka ɓoye a cikin wani babur mai caji, ana kwatanta shi da harin na'urorin sadarwa na Mossad da aka kai wa Hezbolla a farkon shekarar nan, a cewar wani ƙwararre a fannin aikin soji kuma tsohon jami'in hukumar tsaron Ukraine (SBU) Ivan Stupak.

''Dole sai da hukumar leƙen asirin Ukraine ta yanke hukuncin ko za ta harbe shi ne, ko ta saka masa bam, ko kuma ta saka masa guba,'' a cewarsa.

Hukumomin Ukraine ba su ce komai ba a hukumance game da harin.

Jerin sunayen waɗanda za a kai wa hari

Stupak ya ce duk wanda ya shirya ko ya tsara ko ya goyi baya ko kuma ya kai hari kan Ukraine, hukumar tsaron Ukraine mai suna SBU za ta ɗauke shi a matsayin halastaccen wanda za ta kai wa hari.

A cikin jerin sunayen wadanda za a kai wa hari da hukumar tattara bayanan sirri na Ukraine GUR ta wallafa, akwai janar-janar na sojin Rasha da kuma wasu kwamandojin rundunoni - kamar rundunar sojin sama wadanda ke kai hari kan garuruwan Ukraine, da kuma manyan tashohin wutar lantarki.

Amma a duk lokacin da hukumar leƙen asirin ta yanke hukuncin wanda za ta kai wa hari, takan tsaya ta yi nazari kan wasu batutuwa kamar yadda za a kai gare shi da kuma muhimmancin mutumin.

''Wannan aikin na buƙatar ƙwarewa sosai. Irin wannan aikin, wajibi ne ya zama wasu mutane ne za su yi a ƙungiyance,'' a cewar shi.

''Dole ne su gano ko wannan janar din na ɗauke da makamai, su gano wanda ya rako shi, su kuma gano ko hukumar tsaron Rasha sun biyo shi.''

Dole ne jam'ian su yi taka-tsantsan saboda kar a kama su a kan titunan Moscow ɗauke da abubuwan fashewa, ko kuma na'urorin ɗaukar hoton bidiyo da aka saka su gano su - baya ga tsara yadda za su fice daga wurin lami lafiya.

''Akwai wani lokaci da wani jami'in da ke kula da makamancin wannan aikin ya ce min idan ya aika mutanensa irin wadannan ayyukan, yana ganin minti 20 kamar kwana uku ce. Abu ne mai hatsarin gaske da kuma tayar da hankali ga duk wanda ke cikin shirin.''

Bayanan sirri da kuma labaran ƙarya

Hukumar leƙen asiri ta Ukraine ta daɗe tana bibiyar Laftanar Janar Igor Kirillov, shugaban hukumar makamai masu guba ta Rasha, a matsayin wanda take so ta kai wa hari.

A ranar Litinin, hukumar tsaron SBU ta tuhumi Kirillov mai shekara 54 a bayan idonsa da alkahin amfani da makamai masu guba da dama, wadanda aka haramta amfani da su.

A watan Oktoba, Birtaniya ta sanya Kirillov a cikin jerin sunayen wadanda aka saka wa takunkumi. A cewarsu, ya jagoranci amfani da makamai masu guba a Ukraine, kuma ya taka muhimiyyar rawa a matsayin mai magana da yawun gwamnatin Rasha wurin yaɗa labaran ƙarya.

Rasha ta musanta zarge-zargen.

Kirillov ya kuma shirya ɗaya daga cikin sannanun gangamin yaɗa labaran ƙarya kan Ukraine tun lokacin da aka fara yaƙin.

A duk faɗin duniya, an fi saninsa ne kan zarge-zargen da ya yi cewa ƙasashen Yamma na kokarin amfani da makaman ƙare-dangi da ba a amince a yi amfani da su ba a kan Rasha.

Kirillov ya yi ikirarin cewa hedikwatar tsaron Amurka, Pentagon, na ƙoƙarin samun wani adadi na ƙananan dabbobi da ke ɗauke da cutar HIV da cutar hanta ta Hepatitis B domin kaiwa cikin Rasha, kuma ya ce za a saki dandazon sauro masu ɗauke da na'ukan cutuka domin su yaɗa su a cikin Rasha.

Ya zargi Amurka da shirya sabuwar annoba ta hanyar bincike kan yadda za a ƙirƙiro ƙwayoyin cuta na virus, da kuma niyyar shirya fusata Ukraine ta hanyar amfani da abubuwa masu guba kuma su ɗora laifin kan Rasha.

Kirillov ya kuma faɗi maganganu marasa tabbas kan ɗakunan gwaje gwaje kan cutuka masu yaɗuwa da dama da yake zargin Amurka na ginawa a ƙasashe da dama da ke tsohuwar tarayyar Soviet, kuma ya zarge su da daƙile yin bincike kan musabbabin annobar korona.

Ya kuma yi zarge-zarge da yawa. Babu wani shugaba na wani reshe a sojojin Rasha da ya yi magana da ƴan jarida kamar yadda ya yi. A ranar da aka kashe shi ma, kamar yadda ƴan jarida suka ruwaito, Igor Kirillov ya shirya yin magana da ƴan jarida.

Koma-baya ga Putin

Idan aka yi la'akari da yadda majoyoyi masu ƙarfi a hukumar tsaron Ukraine sun ɗauki alhakin harin da aka kai a tsakiyar babban birnin Rasha, na nuna cewa su na da yaƙinin cewa jami'ansu sun samu hanyar ficewa da ta dace.

Kamar dai yadda a ka saba, hukumomin leƙen asiri ba su gaggawa wajen ɗaukar alhakin kai hari domin kare jam'iansu.

Kisan janar din ya faru ne kwana ɗaya bayan taron ma'aikatar tsaro, wanda a ciki Shugaba Vladimir Putin da Ministan Tsaro Addrei Belousov suka yi magana kan yadda sojojin Rasha ke ƙara kusantar yin nasara a yaƙinsu da Ukraine.

Kisan ya kuma zo kwana ɗaya kafin wani shirin siyasa a talibijin na Putin mai suna Direct Line, wanda yake yi duk shekara, inda ake sa ran zai tabbatar wa ƴan Rasha cewa komai na tafiya yadda ya kamata, kuma takunkuman ƙasashen Yamma ba abin da suke yi sai taimaka wa cigaban ƙasar.

Tsohon jami'n tattara bayanan sirri, Stupak, ya ce kisan ba zai sauya al'amuran da ke faruwa a yaƙin da ake yi a Pokrovsk ba, inda dakarun Rasha ke kusantowa - amma za su sa kalaman Putin su zama ba su da wani muhimmanci ga ƴan Rasha wanda zai iya kai ga hare-haren ramuwa a Kyiv.

''Wannan ya nuna rashin ƙwarewar sashin hulɗa da jama'a na Rasha. Ina mamakin yadda jami'an hukumar leƙen asirin Rasha za su kasa bacci saboda yadda shugabanni za su yi ta kiransu a waya suna tambaya iri daya: ya ya aka yi hakan ta faru a Moscow?''.