Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hanyoyi uku da Amurka za ta iya tsoma baki a zaɓen Najeriya
- Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
- Aiko rahoto daga, BBC Hausa
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
Yayin da Najeriya ke tunkarar zaɓen 2027, hankalin ƙasashen duniya na ƙara karkata zuwa yadda za a gudanar da zaɓen da kuma ko za a gudanar da komai cikin lumana.
Daga cikin ƙasashen da ke da muhimmiyar alaƙa da Najeriya akwai Amurka, wadda ke kallon ƙasar a matsayin ɗaya daga cikin manyan abokan hulɗarta a Afirka, musamman a fannin tsaro, tattalin arziki da yaƙi da ta'addanci.
Amma wani abu da ya ƙara ɗaukar hankali shi ne yadda wasu jagororin adawar Najeriya suka fara neman taimakon Amurka da ta sa baki kan abubuwan da suke zargin suna faruwa a siyasar ƙasar.
A baya-bayan nan, mawaƙi David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya yi barazanar kai ƙorafi ga gwamnatin Shugaban Amurka Donald Trump idan ya ga an samu matsala a zaɓen gwamnan jihar Osun.
Gabanin haka kuma tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya yi amfani da kamfanonin kamun kafa da ke hulɗa da gwamnati domin kai ƙorafinsa zuwa ga hukumomin Amurka kan abin da ya kira murƙushe ƴan adawa a Najeriya.
Lamarin ya haifar da cece-ku-ce da musayar yawu tsakaninsa da gwamnatin ƙasar, inda su ma wasu masu sharhi ke ganin irin wannan sam bai dace ba.
"Naƙasu ne ga ƙasashe masu tasowa su miƙa kokon bararsu ga Amurka, ko su ji cewa ƴancinsu ba ya tabbatuwa sai Amurka ta taimaka musu," in ji Farfesa Tukur Abdulkadir, masani kan siyasar ƙasashen duniya
Sai dai tambayar ita ce: me ya sa ƴan siyasar Najeriya ke neman Amurka a irin waɗannan al'amura?
Ba sabon abu ba ne a duniya zargin cewa gwamnatin Amurka na yin katsalandan a harkokin siyasar wasu ƙasashe, musamman a lokacin zaɓe.
A wasu lokuta, jami'an Amurka kan bayyana matsayarsu kan zaɓen wata ƙasa, su yi kira ga gwamnati da ƴan siyasa su mutunta dimokuraɗiyya, ko kuma su yi amfani da takunkumi kan waɗanda ake zargi da take haƙƙin ɗan’adam ko lalata tsarin zaɓe.
A watan Afrilun 2025 ma, ziyarar Mataimakin Shugaban Amurka, JD Vance, zuwa Hungary ta haifar da irin wannan muhawara.
Vance ya je ƙasar ne a daidai lokacin da Firaministan Hungary, Viktor Orbán, ke fafutukar sake lashe zaɓe, kuma rahotanni sun ce ya bayyana cewa ya je ne domin taimaka wa Orbán wajen yaƙin neman zaɓe.
Wannan ya sa wasu suka ɗauki ziyarar a matsayin wata alama ta kai tsaye cewa gwamnatin Shugaba Donald Trump na son ganin Orbán ya ci zaɓen, duk da cewa an yi ta musanta cewa hakan na nufin tsoma baki cikin harkokin cikin gida.
Tasirin Amurka a zaɓuka
Farfesa Tukur Abdulkadir ya ce tarihi ya nuna yadda Amurka ta taka rawa wajen sauya shugabanni a wasu ƙasashe, kuma bai kamata ƙasashe masu tasowa su riƙa ganin cewa ba za su iya kare muradunsu ba sai da taimakon Amurka.
"Duk hakan alamu ne na gazawa."
Duk da haka ya ce zai yi wahala a ce ga inda Amurka ta fito fili ta goyi bayan wani ɗan takara kai tsaye a zaɓen Najeriya.
Ya buga misalin zaɓen shekarar 2015, lokacin da gwamnatin tsohon shugaban Amurka Barack Obama ta nuna goyon bayanta ga gudanar da zaɓe cikin lumana, yayin da ake ganin ta nisanta kanta daga gwamnatin Goodluck Jonathan.
A cewarsa, ɗaya daga cikin hanyoyin da wata ƙasa za ta iya yin tasiri a harkokin wata ƙasa ita ce amfani da takunkumi, ciki har da hana sayar da makamai - kamar yadda ta yi gabanin zaɓen 2015 - , ko kuma yin kalamai da ke nuna rashin amincewa da wata gwamnati.
Ya kuma kawo misalin Iraki, inda Amurka ta nuna rashin goyon bayan Nouri al-Maliki a wani lokaci saboda yadda take kallon salon mulkinsa da manufofinsa.
Haka kuma, ya ce abin da ya faru a Masar bayan hamɓarar da tsohon shugaban ƙasar, Mohamed Morsi, ya nuna yadda Amurka za ta iya sauya matsayinta dangane da shugabannin ƙasashen da take hulɗa da su.
Me ke sa ƴan adawar Najeriya neman taimakon Amurka?
"Ƴan adawa na neman irin wannan agaji idan suna ganin kada a kawo tasgaro ko katsalandan ga dimokraɗiyyar Najeriya," in ji Dr Aliyu Harande, ɗan jarida kuma mai sharhi kan siyasar duniya.
Dr Harande ya ce ƴan adawa kan nemi taimakon wata ƙasa ne musamman idan suka fahimci cewa ba su da isasshen ƙarfi a cikin gida wajen tunkarar matsalar da suke fuskanta.
Ya ce hakan na iya faruwa idan suna tsoron za a yi amfani da ƙarfin gwamnati wajen kawo cikas ga harkar zaɓe ko kuma tauye musu damar yin takara cikin adalci.
Wannan, in ji Dr Harande na daga cikin abubuwan da ke sa wasu ƴan siyasa da ƙungiyoyin farar hula ke neman goyon bayan Amurka idan suna ganin tsarin dimokraɗiyyar ƙasarsu na fuskantar barazana.
Amma ya ce akwai buƙatar a fahimci cewa taimakon ƙasashen waje ba ya zuwa ne ba tare da wata manufa ba.
"Ita Amurka, a mafi akasari, idan aka ga gudummuwar da take bayarwa, na iya zama domin amfaninta."
Sai dai Farfesa Tukur ya ce bai kamata ƴan'adawa a Najeriya su dogara da wata ƙasa wajen cimma manufofinsu na siyasa ba.
"Naƙasu ne ga 'yan adawa su ce za su miƙa buƙatarsu ga Amurka."
A cewarsa, irin hakan na iya raunana ƴancin siyasa, domin idan ɗan siyasa ya dogara da wata ƙasa domin cimma burinsa, hakan na iya haifar da tambaya kan irin ƴancin da yake da shi.
Me zai sa Amurka ta tsoma baki a zaɓen Najeriya?
"Idan Amurka ta zama tana da sha'awa da siyasarku, to akwai abin da take nema wanda zai amfane ta ne, ba wai don ku ƴan ƙasar ba," in ji Dr Aliyu Harande, ɗan jarida kuma mai sharhi kan siyasar duniya.
Shugaban na kafar yaɗa labarai ta GTA Hausa ya ce saboda ƙarfin Amurka da tasirinta a harkokin duniya, matsayinta kan zaɓen wata ƙasa na iya yin tasiri, musamman idan ta fito fili ta nuna damuwa kan yadda ake gudanar da zaɓen ko kuma ta yi kira ga gwamnati da ƴan siyasa su mutunta tsarin dimokraɗiyya.
Ko da yake a ganinsa ba lallai ne irin wannan tsoma baki ya haifar da sakamakon da Amurka ke so a kowane lokaci ba.
"Mafi akasari idan Amurka ta sa baki a zaɓukan wasu ƙasashe, yana tasiri, duk da cewa a wasu lokutan ba ta cika samun nasara ba."
A gefe guda akwai masu ganin tura masu sa ido na ƙasashen duniya domin sanya ido kan zaɓe na iya taimakawa wajen tabbatar da gaskiya da adalci, matuƙar ba a yi amfani da su wajen tsoma baki cikin harkokin ƙasar ba.
Ta waɗanne hanyoyi Amurka za ta iya taka rawa?
Dr Harande ya ce akwai hanyoyi da dama da wata ƙasa mai ƙarfi kamar Amurka za ta iya amfani da su wajen yin tasiri a harkokin zaɓen Najeriya, ba tare da kai tsaye ta bayyana cewa tana goyon bayan wani ɗan takara ba.
Daga cikin hanyoyin akwai:
- Kutse ta intanet: Ya ce ɗaya daga cikin hanyoyin shi ne amfani da fasahar zamani da kafafen yaɗa labarai wajen yin tasiri kan ra'ayin masu zaɓe. Ya kawo misalin yiwuwar kutse ta intanet, inda ƙungiyoyin da ke da alaƙa da wata ƙasa za su iya ƙoƙarin kutsawa shafukan da ake amfani da su wajen gudanar da zaɓe ko kuma yaɗa bayanan ƙarya.
- Amfani da kuɗi: Wata hanya kuma ita ce amfani da kuɗi kan harkokin siyasar ƙasar ƙasa, kamar tallafa wa wasu ƙungiyoyi.
- Ƙungiyoyin sa ido: Ana iya amfani da ƙungiyoyin da ke sanya ido a zaɓuka ta hanyar shirye-shiryen wayar da kan jama'a da sauya ra'ayin masu zaɓe.
Sai dai Farfesa Tukur ya yi gargaɗin cewa irin waɗannan ƙungiyoyin ne ya kamata a yi taka-tsantsan da su, domin "wasu daga cikin ƙungiyoyin da ke shiga ayyukan sanya ido kan zaɓuka na iya kasancewa suna da alaƙa da hukumomin leƙen asiri ko kuma ƙungiyoyin da ke da wata manufa ta siyasa".
Ya ce idan Najeriya na son ƙarfafa dimokuraɗiyyarta, ya kamata 'yan siyasa da sauran masu ruwa da tsaki su fi mayar da hankali kan magance matsalolin cikin gida, maimakon neman taimakon ƙasashen waje.