Lafarin nan da aka hana bizar shiga Amurka a gasar Kofin Duniya da aka kammala a Amurka da Canada da Mexico.
Omar Artan dan Somalia ya isa birnin Salzburg na Austria domin busa wasan UEFA Super Cup tsakanin Paris Saint-Germain da ta ci Cahmpions Lig da kuma Aston Villa da ta ci Europa Lig.
Zai zama dan wata nahiya na farko da zai busa wannan wasa, saboda saka masa da Uefa ta yi na abin da aka yi masa a Kofin Duniya.
Ga wasu nuhinnan abubuwa da ya kamata ku sani game da wasan:
Gasar UEFA Super Cup wasa ne na shekara-shekara da ake yi tsakanin gwarzuwar UEFA Champions League da kuma ta UEFA Europa League.
A bana, za a buga wasan ne tsakanin Paris Saint-Germain, wadda ta lashe Champions League sau biyu a jere kuma ita ce gwarzuwar Ligue 1 ta Faransa, da kuma Aston Villa, wadda ta lashe Europa League karo na farko a tarihinta.
Kungiyoyin biyu za su kara ne a filin wasa na Red Bull Arena da ke birnin Salzburg na kasar Austria, inda za a fara wasan da karfe 8:00 na dare agogon BST ranar Laraba, 12 ga Agusta.
Filin wasan, wanda ke daukar mutane kusan 30,000, shi ne gidan kungiyar RB Salzburg. A yayin gasannin UEFA kuma ana kiransa da Stadion Salzburg.
Ana sauya sunan ne saboda dokokin UEFA da suka shafi tallace-tallace da sunayen masu daukar nauyin gasar, sannan kuma don bambance shi da RB Arena da ke birnin Leipzig na kasar Jamus, wanda ya karbi bakuncin wasan karshe na Europa Conference League na 2026.
A baya, filin wasan ya karbi bakuncin wasu wasannin rukuni na gasar Euro 2008, tare da wasannin Europa League da dama.
Saboda haka, Red Bull Arena na Salzburg na daga cikin fitattun filayen wasa a Turai da suka taba daukar manyan wasannin kasa da kasa da na kungiyoyi.
Wasan zai kasance karkashin jagorancin alkalin wasa Omar Artan na kasar Somalia, wanda aka shirya zai yi alkalanci a Gasar Kofin Duniya ta 2026 amma jami’an kula da iyakoki a Miami suka hana shi shiga Amurka.
Artan yana rike da fasfo na diflomasiyya tare da bizar Amurka mai izinin shiga kasa sau daya kacal, amma duk da haka an hana shi shiga kasar.
UEFA ta bayyana cewa an dauki matakin nada Artan domin wannan wasa ne bayan tattaunawa da Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka CAF.
Artan ne ya lashe kyautar Alkalin Wasa Mafi Kyau na bangaren maza na CAF a shekarar 2025, kuma an sa ran zai zama dan Somalia na farko da zai yi alkalanci a gasar cin kofin duniya.
Nadin nasa domin jagorantar wasan UEFA Super Cup ya zama wata babbar alama ta girmamawa ga kokarinsa da kuma ci gaban alkalancin kwallon kafa a Somalia da nahiyar Afirka baki daya.
Su wane suka taba lashe kyautar a baya?
Daga cikin wasannin UEFA Super Cup guda 50 da aka buga a baya, sau 30 kungiyar da ta lashe babbar gasar kulob-kulob ta Turai (wadda yanzu ake kira UEFA Champions League) ce ta lashe kofin.
An fara gudanar da wannan wasa a hukumance tun a shekarar 1973. Daga lokacin har zuwa shekarar 1999, ana hada gwarzuwa gasar Turai (European Cup/Champions League) ne da ta European Cup Winners' Cup.
Bayan an daina gudanar da gasar European Cup Winners' Cup, sai aka maye gurbinta da ta UEFA Europa League, wanda ya fara fuskantar gwarzuwar Champions League a wasan Super Cup.
-
Real Madrid ita ce kungiyar da ta fi kowacce nasara a gasar UEFA Super Cup, inda ta lashe kofin sau shida.
-
Liverpool ce kungiyar Ingila mafi nasara a wannan gasa, bayan ta lashe kofin sau hudu.
-
Aberdeen ita ce kadai kungiyar Scotland da ta taba lashe UEFA Super Cup.
UEFA Super Cup na ci gaba da kasancewa daya daga cikin muhimman wasannin da ke bude sabuwar kakar wasannin kulob-kulob a Turai, inda yake hada zakarun manyan gasannin nahiyar domin fafatawa kan wani babban kofi na musamman.