Rahotanni sun ce shugaban Amurka, Donald Trump, ya sauya jirgi a kan hanyarsa ta dawowa daga Turkiyya bayan halartar taron ƙasashen NATO, saboda tsoron hari daga Iran.
A cewar jaridar Washington Post, mutane da dama ciki har da wasu ‘yan jarida da ma’aikatan Fadar White House sun yi tunanin cewa Trump yana cikin jirgin shugaban ƙasa, Air Force One, wanda ya hau a gaban kyamarorin talabijin a Ankara.
Sai dai rahoton ya ce jim kaɗan bayan ya shiga jirgin, an sauya shi a ɓoye zuwa wani ƙaramin jirgin saman soja mai suna C32A ta hanyar amfani da motar da ake kai abinci jiragen sama, kafin a tafi da shi zuwa sansanin sojin Amurka da ke Birtaniya.
Jaridar ta ce Fadar White House ta ci gaba da ba da rahotannin cewa shugaban na kan hanyarsa ta komawa Amurka ne a cikin Air Force One, alhali kuwa an sauya jirgin da yake ciki.
Trump ya je Turkiyya ne domin halartar taron NATO cikin wani sabon jirgin alfarma da Qatar ta bai wa Amurka, wanda aka tanada domin amfani da shugaban ƙasa.
Har zuwa yanzu, Fadar White House ba ta fitar da wata sanarwa ba game da rahoton da Washington Post ta wallafa..