Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda Isra'ila ta azabtar da fursunoni Falasɗinawa a kurkukunta
- Marubuci, Alice Cuddy
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 8
Gargaɗi: Wannan maƙalar na ɗauke da bayanai masu tayar da hankali
Fursunoni Falasɗinawa da suka koma Gaza daga Isra'ila sun bayyana wa BBC cewa sun sha azaba kala-kala a hannun sojojin Isra'ila da jami'an gidan yarin ƙasar.
Wani daga cikinsu ya bayyana cewa an riƙa masa azaba da ruwan batir (Acid), sannan a ƙyasta wuta. "Nakan gigice kamar mahaukaci domin in kashe wutar a jikina," in ji Mohammad Abu Tawileh mai shekara 36.
Mun tattauna sosai da mutum biyar da aka sako, waɗanda dukkansu aka kama a Gaza kimanin wata ɗaya bayan Hamas da wasu ƙungiyoyin sun kashe kusan mutum 1,200 a Isra'ila, sannan suka yi garkuwa da aƙalla mutum 251.
An tsare mutanen ne a ƙarƙashin dokar sojin Isra'ila, wadda ta ba ƙasar damar daɗewa tana tsare da mutanen da take zargi suna barazana ga ƙasar ba tare an gabatar da su a kotu ba.
Mutanen sun ce an zarge su ne da alaƙa da Hamas, inda aka riƙa tambayar su inda aka ɓoye waɗanda aka yi garkuwa da su, da neman su fallasa hanyoyin ƙasa. Amma an gane cewa ba su da hannu a harin 7 ga Oktoban 2023 - wanda shi ne ƙa'idar da Isra'ila ta saka domin sakin fursunoni a yarjejeniyar tsagaita wuta da Hamas a Gaza.
Wasu daga cikin waɗanda aka saka akwai waɗanda suka yi shekaru da dama a gidan yari saboda laifuka daban-daban. Mun kuma tambayi rundunar tsaron Isra'ila IDF da jami'an tsaron gidan yarin Isra'ila wato IPS ko an yanke musu hukunci ko kuma akwai zargin da ake musu, amma ba mu samu amsoshin tambayoyinmu ba.
A jawabin da suka gabatar akwai:
- Dukkansu sun ce an musu tsirara, an rufe musu fuska, sannan sun sha duka
- Wasu sun ce an musu azaba da lantarki, an tura musu karnuka, sannan ba a bari suna ganin likita
- Wasu sun ce a gabansu wasu fursunonin suka mutu
- Wani ya ce ana cin zarafin fursunoni
- Ɗaya ya ce an watsa masa ruwan guba sannan aka ƙyasta wuta
Mun ga wani rahoto da wani lauya da ya ziyarci biyu daga cikinsu a gidan yari ya fitar, kuma mun zanta da ma'aikatan jinya da suka musu jinya bayan sun koma gida.
BBC ta tura saƙon neman martani ga IDF cike da bayanan zargin da mutanen suke yi, da cikakken bayanansu.
A wata sanarwa, duk da cewa IDF ba ta amsa zargin ɗaya bayan daya ba, amma ta ce "tana watsi da dukkan zarge-zargen da ake mata na tauye haƙƙin fursunonin."
Sai dai ta ce wasu daga cikin bayanan da BBC ta bayar za su miƙa "ga hukumomin da suka dace domin yin nazari." sannan ta ƙara da cewa daga ciki, "akwai wasu bayanan da ba su fito da kyau ba, don haka ba za ta iya tantancewa."
Sannan ta ƙara da cewa IDF ba ta wasa da duk wani mataki da ya saɓa da dokokin ƙasar.
Dr Lawrence Hill-Cawthorne, ɗaya daga cikin daraktocin cibiyar tabbatar da shari'a ta duniya a jami'ar Bristol ya ce bayanan da mutanen suka bayar ya saɓa da dokokin duniya da na Isra'ila.
Falasɗinawa biyar da muka tattauna da su sun koma gida ne a farkon wannan shekarar a cikin waɗanda aka saka saboda yarjejeniyar tsagaita wuta.
Suna cikin Falasdinawa 1,900 da aka sako domin musaya da Isra'ilawa 33 - takwas waɗanda suka rasu da waɗanda suke raye 25 - kuma wasu daga cikinsu sun ce an ci zarafinsu, kuma an bar su da yunwa lokacin da suke hannun ƴan Hamas.
Dukkan mutum biyar ɗin da muka zanta da su sun ce tun daga kama su ake gana musu azaba - lokacin da aka musu tsirara, aka rufe fuskokinsu, sannan aka tafi da su ana bugu.
Ya faɗa mana cewa sojoji suna hada sinadaran wanki a wata tukunya, sai a danna kansa a ciki. Bayan amfani da sinadaran, sai su ƙyasta wuta. Sai in gigice kamar mahaukaci a ƙoƙarin da nake yi na kashe wutar. Wutar sai ta faɗaɗa daga kai zuwa ƙafa, sai kuma su cigaba da bugu na da gindin bindiga," in ji shi.
Sai "suka cigaba da watsa min gubar acid. Sai da na yi kusan kwana ɗaya da rabi ana watsa min ruwan acid," in ji shi.
Ya ce daga baya ne sojojin suka watsa masa ruwa, suka tafi da shi Isra'ila aka kai shi asibiti.
Gargaɗi: Hoton da ke ƙasa yana tayar da hankali
Lokacin da BBC ta gana da Mista Abu bayan an sako shi, bayansa a caɓe yake da alamun ƙuna, sannan yana fama da ciwon ido.
BBC ba ta samu ganawa da wanda ya ga lokacin da aka gana wa Abu azaba ba, amma likitan ido da ya duba shi bayan ya dawo ya tabbatar da cewa an watsa masa guba a ido, sannan ya ce ganin Abu ya yi kaɗan saboda ko dai gubar ko kuma azaba.
Mun nuna wa likitocin Amurka da dama hotunansa, kuma sun ce sun yi daidai da wanda ya sha irin azabar da Abu ya bayyana, duk da cewa sun ce akwai abubuwan da ba za su iya gane daga hotuna ba.
BBC ta miƙa wannan bayanin ga IDF, inda aka ba su kwana biyar domin su yi martani. Ba ta bayar da gamsasshiyar amsa game da zargin Mista Abu ba, amma ta ce duk wani abu da ya saɓa da dokokinsu ba sa ɗaukarsa da wasa.
Ta ce za ta yi nazarin wasu daga cikin zarge-zargen da Mista Abu ya tura.
Sauran waɗanda muka zanta da su ma sun bayyana irin azabar da aka gana musu a lokacin da aka kama su.
"Sun saka mana ankwa ne suna ta bugun mu, babu wanda zai ba ka ruwan sha," in ji Abdul Karim Mushtaha mai shekara 33 wanda ke aiki a mayankar kaji da aka kama a watan Nuwamban 2023.
Biyu daga cikin sun ce ana barinsu a waje a cikin sanyi, wasu guda biyu kuma sun ce sojojin Isra'ila sun sace musu wayoyi da kuɗi.
Dukkan waɗanda muka zanta da su sun ce an kai su barikin sojojin Isra'ila ne na Sde Terman, inda Mr Abu ya ce an masa jinya.
Wani da muka tattauna da shi ya ce an gana musu azaba a hanya. Ya ce a ɓoye sunansa saboda tsoron abin da zai faru, don haka muke kiransa "Omar".
Ya ce sojojin Isra'ila sun riƙa kiransu "ƴaƴan aladu."
Uku daga cikin waɗanda muka zanta da su sun ce ana amfani da kare domin tsoratar da su a Sde Teiman.
"Za a mana bugu a duk lokacin da suka ɗauke mu daga asibiti zuwa wajen amsa tambayoyi - suna turo mana karnuka alhali muna cikin ankwa," in ji Mr Abu Tawileh.
BBC ta tambaya IDF kan zargin ko tana amfani da karnuka wajen tsoratar da waɗanda suka kama, inda ta ce, "ba mu amincewa da amfani da karnuka wajen tsoratar da wadanda suke riƙe."
"Mukan durƙusa daga ƙarfe biyar na safe zuwa ƙarfe 10 na dare lokacin da za mu yi barci," in ji Mr Abu.
Hamad al-Dahdou, wani wanda muka tattauna da shi ya ce idan suna bugunmu, sun fi neman kanmu da kunne da ido.
IDF ba ta ce komai kan wannan zargin ba.
Omar ya ce an ci zarafinsa a Ketziot.
"Sun cire mana tufafi, sannan su aikata baɗala. Suna tursasa wasu su ci zarafin wasu, na ga wannan da idona. Ba wai saduwa suke yi ba, ana tursasa wani na yi wasa tare da tsotsar gaban wani, kuma dole ne ka yi."
BBC ba ta samu irin wannan ƙorafin daga wani ba, amma ƙungiyar fursunoni Falasɗinawa ta Palestinian Prisoners Society ta ce zargin cin zarafi a fursunan Ketziot ba sabon abu ba ne.
BBC ta tambayi IPS zargin cin zarafi, lamarin da ta ce ba ta da masaniya.
Omar ya ce an kuma ta dukansu a gidan yarin Ketziot.
"Bayan azaba, wani dare haka aka yi ta dukana har na yi laushi. Sai wasu ɗauke ni suka kai mu wane wuri.
"Sai su mana tsirara, su riƙa dukanmu, suna ce mana za su dandaƙe mu," in ji shi.
Suna faɗa mana cewa ana "dukanmu ne domin a karya mana ƙasusuwa."
"Gaskiya azabar ta yi yawa," in ji shi.
"Sai da kaina ya kumbura saboda duka," in ji Mushtaha.
A wani rahoto da wani lauya wanda ya ziyarci Mr Mushtaha and Omar a Ketziot a watan Satumba, "yawancin fursunonin sun sha wahala da azaba da ƙuna a hannu da ɗuwawu, kuma inda suke zama babu tsafta."
Omar ya ce ana dukan fursunoni idan suka buƙaci zuwa ganin likita.
Dukkan waɗanda aka tsare ɗin ba su samun isasshen abinci da ruwan sha a lokacin da suke tsare.
Mista Mushtaha ya ce ana ajiye abincinsu a waje ne tsuntsaye su fara ci kafin su ci.
Ya ce jami'an tsaron Isra'ila suna shigowa ɗakunansu, suna watsa musu barkonon tsohuwa.
"Sai mu shaƙe mu kasa numfashi, kuma haka muke zama mu yi kwanaki," in ji Ahmed wanda aka tsare a sashen matasa na gidan yarin.
"Ba sa ko damuwa cewa mu yara ne, suna mana azaba ne kamar ƴanbindiga da suka kai harin 7 ga Oktoba."
Mutum biyu da muka zanta da su sun bayyana yadda fursunoni biyu suka mutu a gabansu a kurkukun Sde Teiman da Ketziot - ɗaya ta hanyar duka, ɗaya kuma saboda rashin samun kula.
Aƙalla Falasɗinawa fursunoni 63 - 40 daga cikinsu ƴan Gaza - ne suka rasu a gidajen yarin Isra'ila tun bayan harin 7 ga Oktoban 2023, kamar yadda ƙungiyar fursunoni ta Palestinian Prisoners Society ta shaida wa BBC.
Sun ce an cigaba da gana musu azaba har zuwa lokacin da za a sake su a watan Fabrairu.
"Ranar da za a sake mu ma sun gana mana azaba. Sun ƙara ɗaure ankwar da ke hannunmu, sannan suka riƙa tura mu," in ji Mushtaha.
"Sun riƙa faɗa mana cewa idan kuka yi aiki da Hamas za mu neme ku mu kashe ku. Za mu harba muku makami mai linzami ya tarwatsa ku."
Ahmed mai shekara 17 ma ya ce azabar ta ƙara zafi ne bayan yarjejeniyar tsagaita wuta, inda "suka ƙara ƙaimi wajen gana mana azaba kafin mu fita."
Omar ya ce ba su samu sauƙi ba, har sai lokacin da aka miƙa su a hannun jami'an ƙungiyar agaji ta Red Cross.