Shaw zai ci gaba da taka leda a United zuwa 2027

Asalin hoton, Getty Images
Mai tsaron baya, Luke Shaw ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da wasa a Manchester United zuwa karshen Yunin 2027.
Mai shekara 27 zai ci gaba da wasa a Old Trafford sama da kaka 10, bayan da ya koma United daga Southampton a 2014.
Shaw na taka rawar gani a United a kakar nan karkashin Erik ten Hag, wanda ya yi wasa 36 a dukkan fafatawa da cin kwallo daya ya bayar da shida aka zura a raga.
Shaw wanda ya buga wasa 249 a Manchester United ya sha suka karkashin kociya, Jose Mourinho.
Bayan da United ta kori Mourinho ta nada Ole Gunner Solskjaer ya koma buga karawa sosai, sannan ya dora a karkashin Ten Hag, wanda ke tsare baya daga gefen hagu.
Shaw ya yi wa Ingila wasa 29 da cin kwallo uku har da wadda ya fara ci a Euro 2020 a wasan karshe da Italiya.








