An yi gumurzu tsakanin Bahagon 'Yan sanda da Dogon Magaji

An wallafa

Bahagon Shagon 'Yan sanda da Dogon Magaji sun dambata a gidan wasa na Ali Zuma da ke DeiDei a Abuja, Najeriya ranar Lahadi.

Bahagon 'Yan sanda daga Arewa da Dogon Mgaji Guramada sun yi turmi uku ba kisa, amma a turmin farko suka fi yin dambe.

Turmi na biyu da na uku ba wanda ya kai duka, daga nan alkalin wasa Sanin Gidan dan Kande ya raba su.

Sauran sakamakon wasannin da aka buga, Zazu daga Kudu da Ramadan Shagon Autan dan Bunza daga Arewa ba kisa.

Shi kuwa dan Bichi Shagon Inda daga Arewa ya buge Bahagon Shagon Alabo daga Kudu a turmin farko.

Haka damben na gaba, Autan Ali Kanin Bello daga Jamus ya yi nasara a kan Pasto Shagon Mai Takwasara Guramada.

Shi kuwa Shagon Inda daga Jamus buge Matawallen Kwarkwada daga Kudu ya yi a turmi na uku.

Wasa tsakanin Shagon Kosilaye daga Kudu da Shagon Bahagon Musan Kaduna daga Jamus ba kisa a turmi biyun da suka yi.