Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Chelsea ta doke West Ham gida da waje a Premier League
Chelsea ta yi nasarar doke West Ham United 2--1 a karashen wasan mako na 24 a Premier League da suka kara ranar Litinin a Stamford Bridge.
West Ham ce ta fara cin ƙwallo ta hannun Jarrod Bowen daf da za su je hutun rabin lokaci a wasan na hamayya na ƴan birnin Landan.
Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Chelsea ta farke ta hannun Pedro Neto, sannan ta kara na biyu, sakamakon da Aron Wan Bissaka ya ci gida.
Chelsea ta je ta doke West Ham 3-0 a wasan farko a Premier League a bana ranar 21 ga watan Satumbar 2024.
Da wannan sakamakon Chelsea ta koma mataki na huɗu a kan teburin Premier League da maki 43.
Hakan ya sa Manchester City ta yi kasa zuwa mataki na biyar da maki 41, iri ɗaya da na Newcastle United ta shidan teburi.
Chelsea za ta je gidan Brighton ranar Asabar 8 ga watan Fabrairu, domin buga FA Cup, daga nan ta sake karawa da Brighton a Premier League ranar 14 ga watan Fabrairu.
Sakamakon wasannin mako na 24 a Premier League:
Ranar Asabar 1 ga watan Fabrairu
- Nottingham Forest 7 - 0 Brighton
- Everton 4 - 0 Leicester City
- Ipswich 1 - 2 Southampton
- Bournemouth 0 - 2 Liverpool
- Newcastle 1 - 2 Fulham
- Wolverhampton 2 - 0 Aston Villa
Ranar Lahadi 2 ga watan Fabrairu
- Manchester United 0 - 2 Crystal Palace
- Brentford 0 - 2 Tottenham
- Arsenal 5 - 0 Manchester City
Ranar Litinin 3 ga watan Fabrairu
- Chelsea 2 - 1 West Ham