Malamar da dalibinta mai shekaru shida ya harba na samun sauki

Abby

Asalin hoton, ABBY ZWERNER/FACEBOOK

An wallafa

Hukumomi a jihar Virginia da ke Amurka sun ce malaman firamaren nan da dalibinta dan shekara shida da haihuwa ya harba da bindiga, na samun sauki a asibiti. Ranar Juma'a dalibin ya harbi malamar tasa yayin da suke sa-in-sa a makarantar Richneck Elementary da ke Newport News. Hukumomi sun bayyana sunan malamar da Abby Zwerner, kuma sun ce ta samu raunuka masu muni biyon bayan harbi da yaron ya mata.

Sai dai har yanzu ba bu bayanan yadda aka yi yaron dan shekara shida ya iya mallakar bindiga, da kuma yadda aka yi ya iya shiga da ita makaranta a sace. An sanar da rufe makarantar ta Richneck daga gobe Litinin, yayin da bincike ke kara fadada. Mai garin na Newport News ya ce sun yi takaicin faruwar lamarin, kuma lokaci ya yi da yan siyasa a Amurka za su ja layi daga mallakar bindiga a kasar. A yanzu yaron na ci gaba da zama hannun jami'an tsaro har sai yadda hali ya yi. Doka a jihar Virginia ta haramta gurfanar da kananan yara masu shekaru shida a gaban kotu. Sai dai alkali na da zabin kwace yaron daga hannun iyayensa, domin gwamnati ta bashi horo na musamman da kuma saka ido kansa sosai.