An tsare dan shekara shida da zargin harbin malamarsa da bindiga a Amurka

.

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Yan sanda a birnin Newport News na jihar Virginia a Amurka na tsare da wani karamin yaro dan shekara shida, bisa zargin harbin malamarsa da bindiga.

Lamarin ya faru ne a makarantar Firamare ta Richneck Elementary, bayan sa-in-sa tsakanin dalibin da malamar tasa.

Jiya da daddare ne yan sanda suka samu rahoton harbi a makarantar firamare ta Richneck Elementary, kuma ba tare da bata lokaci ba suka kai jiki.

Anan suka fahimci cewa dalibi ne dan shekara shida ya yi amfani da bindiga ya harbi malamarsa.

Sanarwar yan sandan ta kara da cewa harbin ba na kuskure bane.

Malamar wadda kawo yanzu ba a bayyana sunanta ba na jinya a asibiti kan raunukan da ya mata.

Rahotanni sun ce an samu rashin jituwa ita da dalibin nata ne, kuma yayin sa-in-sa karamin yaron ya yi yunkurin hallaka malamarsa tasa.

Yan sandan sun ki fitowa su bayyana nau'in bindigar da ya yi harbin da ita.

Yanzu haka an sanar da matakin rufe makarantar ta Richneck Elementary daga ranar Litinin, yayin da ake ci gaba da bincike.

Mai garin na Newport Phillip Jones, ya ce suna bakin ciki da faruwar wannan mummunan al'amari, kuma za su yi duk mai yiwuwa wurin dakile afkuwar hakan a gaba.

Ba sabon abu ba ne kai harin bindiga a makarantun Amurka, kasar da yan siyasa ke ci gaba da samun rabuwar kai kan ikon mallakar bindiga.

Sai dai ba a saba ganin karamin yaro da yunkurin kisa da bindiga ba a cikin makaranta.