Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Saka ne gwarzon Arsenal na watan Agusta
Bukayo Saka ne ya lashe ƙyautar gwarzon ɗan wasan Arsenal na watan Agusta.
Magoya bayan ƙungiyar ne ke kaɗa kuri'ar wanda ya fi ƙwazo a Gunners a wata-wata, inda David Raya ya yi masa na biyu.
Saka ya zama na biyu da ya bayar da ƙwallo aka zura a raga a wasa uku da fara kakar bana a tarihi.
Shi ne ya bai wa Kai Havert ƙwallon da ya ci Wolves da wadda ya zura a ragar Brighton da wadda ya bai wa Thomas Partey ya ci Aston Villa.
Thierry Henry ne mai rike da wannan bajintar da ya yi wa Gunners a 2004/05.
Haka kuma Saka ɗan wasan tawagar Ingila ya ci ƙwallo da fara kakar bana, wanda ya zura ɗaya a ragar Wolves ranar 17 ga watan Agusta.
Wannan shi ne karo na takwas da Saka ya lashe ƙyautar da ake yi duk wata-wata har da biyu a bara a watan Satumba da Fabrairun 2024.
Arsenal tana mataki na huɗu a teburin Premier League da maki bakwai, iri ɗaya da na Brighton ta uku, bayan wasa uku da fara kakar bana.
Wasannin da Arsenal za ta yi cikin watan Satumba
Premier League ranar Lahadi 15 ga watan Satumbar 2024
- Tottenham da Arsenal
Champions League ranar Alhamis 19 ga watan Satumbar 2024
- Atalanta da Arsenal
Premier League ranar Lahadi 22 ga watan Satumbar 2024
- Man City da Arsenal
English League Cup ranar Laraba 25 ga wwatan Satumbar 2024
- Arsenal da Bolton
Premier League ranar Asabar 28 ga watan Satumbar 2024
- Arsenal da Leicester