Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zaben Kenya: Yadda ake biyan wadanda suka yi fice a kafofin sada zumunta don jan hankalin jama'a
Amfani da kafofin sada zumunta domin jan hankalin mutane na ci gaba da bunkasa kuma ya koma wani fannin kasuwanci ga matasan Kenya, inda suke samun kudi sosai sakamakon karuwar 'yan siyasa da ke amfani da su.
“Mutane sun san cewa kai mai gabatar da maudu’i ne ta hanyar amfani da maudu'ai, kowa a Twitter ya san ana biyanka kudi don ka yi wa dan siyasa aiki," in ji Nick, marubuci mai zaman kansa daga Nairobi kuma wani da ke son ya zama wanda ke da tasiri a kafofin sada zumunta.
"Amma 'yan siyasa ba za su yarda a bainar jama'a cewa sun biya wani mai tasiri don yada sakonnin yakin neman zabensu ba. Suna kokarin ganin kamar ba su da wata alaka da su."
Yayin da za a yi fafatawa mai zafi a zaben shugaban kasar Kenya a ranar 9 ga watan Agusta, mutane da dama sun nuna damuwa cewa tsarin amfani da wadanda suka yi fice a kafofin sada zumunta na iya haifar da magudi da kuma yada labarai masu cutarwa.
Nick, wanda shekarunsa ba su wuce 20 ba ya fara tallace-tallace a shafukan sada zumunta don samun karin kudi yayin karatu ko neman aiki.
Yayin da ya samu mabiya, kamfanoni da gidajen talibjin da mutanen da ke son su kaddamar da wata sabuwar haja ko wani sabon abu kan neme shi don tallata su a shafin Tweeter.
An kuma ba shi wasu ayyukan siyasa inda ya rika samun kudi da yawansu ya kai 1,000 na kudin Kenya - kimanin fan bakwai - domin ya yi aiki na sa'o'i kadan wanda albashi ne mai kyau idan aka kwatanta da wasu ayyuka.
Nick ya ce ya fi son ya tallata kayayyakin da yake so maimakon na 'yan siyasa amma yana tura sakon goyon bayan dan takara a shafin Tweeter duk da cewa ba zai zabe shi ba.
"A ra'ayina, in dai ba su tallata wani abu maras kyau ko na tashin hankali ba ko na kabilanci ban damu ba. Wane ne ba ya son karin kudi?
Sai dai wannan babbar harka ce ga jam'iyyun siyasa da 'yan takara.
"Wannan babban aiki ne a lokacin siyasa saboda ana musayar biliyoyin kudi," in ji Gordon Opiyo, wani masanin siyasa, wanda ke aiki tare da masu goyon bayan mataimakin shugaban kasa kuma dan takara William Ruto.
Gordon ya ce: "Masu goyon bayan dan takara da aka dora wa alhakin shirya yakin neman zabe, aikinsu na farko shi ne daukar wadanda suka yi fice a shafukan sada zumunta aiki - wadanda ake kira microinfluencers - da Ingilishi masu mabiya tsakanin 10,000 da kuma 500,000. Daga nan sai su kirkiro wani dandali tare da zayyana dabaru inda ake ba da umarnin amfani da maudu'ai da hotuna da kuma wuraren magana."
Manufarsu ita ce su rika sa ido akan duk wani bayani da ya shafi dan takara ko maudu’i , kuma bas ai sun dogara akan kafofin yadda labarai ba watau za su iya zuwa kafofin sada zumunta kai tsaye.
Masana sun ce kusan duk wani yunƙuri na samun alamar siyasa mai yiwuwa ana biyan kuɗi.
"Idan ka ga abu ciki tare da hashtag, ka san wasan ƙarshe shine an yi haka ne domin ya samu karbuwa," in ji Brian Obilo, wanda ya bincike akan waɗannan abubuwa a madadin cibiyar sadarwa ta Mozilla Foundation da ke Kenya.
"Suna ikirarin cewa ana amfani da tambarin ne don tara magoya baya, amma idan ka duba asusun ajiyar da ke fitar da tags, za ka ga asusun yana da hannu wajen yada labaran karya ta shafin intanet. Za ka san wuka da naman a hannu wani."
'Yan siyasa na nesanta kansu daga wannan harka," in ji Gordon.
"Mafi yawan masu tallafawa galibi ana ware su ne, ba za ku taba samun su da wani kwantiragi na yau da kullun ba."
A cewar Code for Africa, wata tawagar da ke gudanar da bincike kan kalaman ƙiyayya da kuma yaƙin neman zaɓe na hadin gwiwa, maudu'in RutoMalizaUfungwe (watau "[Mataimakin Shugaban Ƙasa] Ruto ka gama wa'adinka kuma ya wuce kurkuku") ita ce ta ɗaya. abubuwan da ke faruwa a Twitter bayan an tallata su ta hanyar amfani da shafukan karya.
Da yawa daga cikinsu sun yi tsokaci kan tashin hankalin da ya biyo bayan zaben 2007, wanda ya kai ga shari'ar Mista Ruto a Hague, kuma wasu sakonni na kunshe da kalaman nuna kiyayya.
Kamar dai yadda aka yi a shekarun baya, an yi kokarin hada kai don nuna shakku kan ingancin hukumar zaben kasar.
Isaac yana son yin aiki a siyasa. Ya kasance yana tallata yakin neman zaben Mista Ruto kuma ya ce an biya shi kudi domin ya rika wallafa sakonni 30 a rana.
A watan da ya gabata ya tura wani sako yana zargin cewa ba za a iya amincewa da shugaban hukumar zaben kasar ba.
A watan Yuni, shafin Twitter ya dakatar da wasu shafuka 41 da ke da hannu wajen tallata irin wannan maudu’in da ke nuna Mista Wafula Chebukati, shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (IEBC), yana goyon bayan Mista Ruto, saboda keta manufofinsa na magudi da kuma satar bayanan sirri.
Twitter ya shaida wa BBC cewa ya haramta "kokarin da wasu sukeyi na amfani da shafin don yin magudi ko kawo cikas ga harkokin jama'a, ta hanyar rarraba bayanan karya ko yaudara a kan kaidojin zabe".
Wannan dai wani bangare ne na yakin da ake yi na bata sunan cibiyoyi, wanda kuma yana cikin abubuwan da suka ta'azzara tashe-tashen hankula a zabuka a baya, in ji Allan Cheboi na Afrika. Kungiyar ta lura da kokarin bata sunan hukumar ta IEBC akan TikTok da kuma wasu labaran da ba a bayyana sunansu ba da suka yadu a WhatsApp.
Sai dai duk da cewa wannan harka ce ta samun kudi amma akwai wasu da suka yi fice a shafukan sada zumunta da suka nuna rashin jin dadinsu akan wadanda suke yi wa aiki .
"Muna iya yada bayanan karya game da wani dan siyasa, kuma wasu kwanaki suna yaba wa abokan hamayyarsu. Ya danganta da wanda ke biyan kudin aikin," in ji Alex, ba ainihin sunansa ba, ta WhatsApp. Bayan da aka dakatar da shafinsa na Twitter yana jin takaicin rashin iya aiki.
"Kamar itace. Mu kawai ganye ne, me yasa na ce haka? Domin ana iya maye gurbin masu tasiri a kowane lokaci."
Kamar Alex, Nick ba shi da sha'awar wannan layin na aiki. Ya ce ayyukan siyasa sun yi kaurin suna saboda wani muhimmin dalili.
"Akwai yuwar cewa ba za a biya ku ba. Ba daidai ba ne da wani aikin talla," in ji shi. "Na farko dai ba ka yarda da abin da kake yi ba, don kudi kawai kake yi kuma wannan kudi bazai zo ba, ni kaina ba mai son hakan ba ne."