Lukaku na shirin komawa Roma

An wallafa

Dan wasan gaba na Chelsea, Romelu Lukaku na shirin komawa kungiyar kwallon kafa ta Roma ta kasar Italiya a matsayin aro na tsawon kaka daya.

Yarjejeniyar ta hada da kudin daukan aro fam miliyan takwas, kuma Roma za ta biya albashin dan kasar Belgium ɗin mai shekara 30.

Inter Milan ta yi fatan dawo da Lukaku bayan zaman aro da ya yi kakar da ta gabata ganin cewa yanzu dan wasan ba ya cikin tasrin Mauricio Pochettino a Chelsea.

Amma Lukaku ya samu saɓani da koci Simone Inzaghi sakamakon rashin farawa da shi a wasan karshe na gasar zakarun Turai.

Ita ma Juventus ta so dauko Lukaku amma ta kasa yin sauye-sauyen da ake bukata a kungiyar.

Har yanzu akwai wasu bayanai da za a kammala amma dukkan alamu sun nuna cewa dan wasan ya kulla yarjejeniyar komawa Italiya.

Komawarsa Roma na nufin Lukaku zai sake haduwa da Jose Mourinho wanda ya rarrashe shi ya koma Manchester United a madadin Chelsea lokacin da ya koma Old Trafford daga Everton a 2017.

Lukaku ya koma Chelsea daga Inter Milan kan fam miliyan 97.5 a watan Agustan 2021 kan yarjejeniyar shekaru biyar, amma ya gaza kafa kansa a kungiyar kuma wannan kakar yana atisaye ba tare da sauran 'yan tawagar kungiyar ba.

Ya zura kwallo 15 a wasa 59 a Blues a zama biyu da ya yi a kungiyar.