Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Barca ta caskara Royal Antwerp a Champions League
Barcelona ta doke Royal Antwerp 5-0 a wasan farko a rukuni na takwas a Champions League da suka kara ranar Talata a Sifaniya.
Tun a minti na 11 da fara wasa, Joao Felix ya ci ƙwallo, minti takwas tsakani Robert Lewandowski ya ci na biyu, sai kuma Jelle Bataille, wanda ya ci gida.
Bayan komawa daga hutu, a zagaye na biyu ne kungiyar Sifaniyan ta ƙara ƙwallo na hudu ta hannun Pablo Gavira, yayin da Felix ya ci na biyar kuma ƙwallo na biyu a fafatawar.
Daya sakamkon wasan ƙungiyoyin da ke rukuni na takwas, FC Porto ta je ta ɗura kwallo 3-1 a ragar Shakhtar Donesk.
Wannan shi ne wasa na uku da suka ƙara a tsakani, inda Barcelona ta ci biyu kenan, ita kuwa Royal Antewerp ta yi nasara a ɗaya.
Ranar 4 ga watan Oktoba, Royal Antwerp za ta karɓi baƙuncin Shakhtar Donetsk a wasa na bi-biyu a rukuni na takwas, inda a ranar Barcelona za ta ziyarci FC Porto.
'Yan wasan Barcelona 21 da koci, Xavi Hernández ya bayyana don karawa a wasan.
'Yan wasan Barcelona:
Ter Stegen, Joao Cancelo, Balde, I. Martínez, Gavi, Ferran, Lewandowski, Raphinha, Iñaki Peña, João Félix, Christensen da kuma Marcos A.
Sauran sun hada da Romeu, S. Roberto, F. De Jong, Gündoğan, Kounde, Astralaga, Lamine Yamal, M. Casadó da kuma Fermín.