Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wasu batutuwan kan wasan Man United da Barcelona
Barcelona ta ziyarci Manchester United ranar Alhamis, domin buga wasa na biyu a neman gurbin ci gaba da Europa League.
Duk wadda ta yi nasara za ta kai matakin 'yan 16 da za su ci gaba da wasannin Zakarun Turai a Europa League a kakar nan.
Ranar Alhamis kungiyoyin biyu suka tashi 2-2 a Nou Camp a wasan farko.
Wannan shine karo na shida da Barcelona za ta ziyarci Old Trafford, inda wasa biyu ne United ta yi nasara.
Farko Barcelona ta ci United 2-0 a Cup Winners Cup a 1983/84 a Nou Camp, amma a wasa na biyu aka doke ta 3-0 a Old Trafford, inda Bryan Robson ya ci biyu da Frank Stapleton mai daya.
Daga nan suka yi canjaras biyu a karawar cikin rukuni - United ta doke Barcelona 1-0 ta hannun Paul Schools a daf da karshe a kakar 2008.
Sai dai Barcelona ta yi nasara a kan United a quarter finals a kakar 2019, inda Luke Shaw ya ci gida a Old Trafford.
Wasannin baya da Barcelona ta ziyarci Old Trafford:
1983/84 Cup Winners' Cup
- Man Utd 3-0 Barça
1994/95 Champions League
- Man Utd 2-2 Barça
1998/99 Champions League
- Man Utd 3-3 Barça
2007/08 Champions League
- Man Utd 1-0 Barça
2018/19 Champions League
- Man Utd 0-1 Barça
Labarin da ya shafi kungiyoyin
Xavi ya ajiye wasu fitattun 'yan wasa a karawar da Barca ta ci Cadiz 2-0 a karshen mako a La Liga.
Sai dai Ousmane Dembele ba zai buga wasan ba, sannan an dakatar da Gavi daga buga karawar.
Sai dai an je da Ronald Araujo Ingila, wanda zai yi wasa na 100 a Barcelona.
Haka kuma ana sa ran kyaftin Sergi Busquets zai yi wasan na hamayya.
Manchester United za ta yi karawar ba tare da Van de Beek da Eriksen da kuma Martial ba, sannan ana auna koshin lafiyar Antony.
Ranar Lahadi United ta doke Leicester City 3-0 a Old Trafford a gasar Premier League karawar mako na 24.