Sau nawa ya kamata ka yi bahaya a rana?

Asalin hoton, Emmanuel Lafont/BBC
- Marubuci, Jasmin Fox-Skelly
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 7
A bisa tsari, bahaya wani abu ne da ake yi sau ɗaya a rana.
Kai sau uku kake yi a rana ko kuwa? zuwa bayangida wani gagarumin abu ne da ba kasafai yake faruwa ba? Kuma menene iya yawan bahayar da kake yi yake bayyanawa game da lafiyar ka? Zauna ka natsu ka koyi kimiyar bahaya.
Yawan zuwa bahaya ya bambanta ne daga mutun zuwa mutum. Duk lokacin da muka ci abinci, babban hanjinmu yana matsewa ya tura abincin zuwa wurin da zai narke.
Hakan na kai wa ga sakin wasu sinadarai da ke sanya buƙatar yin bahaya. Wasu daga cikinmu sun koyi danne wannan buƙatar wanda hakan ke nufin yin bahaya sau ɗaya a rana ko ƙasa da haka ya zame musu jiki.
''Dukkaninmu muna nuna kamar abubuwa sunyi mana yawa bamu da lokacin yin bahaya,'' in ji Martin Veysey, wani likitan kayan ciki a asibitin Canberra da ke Australia.
Bisa al'ada, ana ganin cewa yin bahaya sau ɗaya a rana alama ce ta lafiyar ciki. Sai dai a baya ba a san menene ''daidai'' ba idan aka zo maganar bahaya. Wani bincike ya taɓa bayyana cewa yin bahaya sau ɗaya cikin makonni ko watanni da kuma yin bahaya sau 24 a rana za a iya cewa daidai ne.
Sai dai saboda binciken masana kimiyya kamar Ken Heaton, wani likita a asibitin Bristol Royal da ke Birtaniya, yanzu mun san gaskiya.
A ƙarshen shekarun 1980, Keaton da abokan aikinsa sun bibiyi mazauna gabashin Bristol, suna tambayar su - sau nawa kuke bahaya?
Sakamakon binciken ya nuna bambanci mai girma tsakanin yadda mutane ke bahaya. Sai dai wanda aka fi samu shi ne bahaya sau ɗaya a rana, kuma kashi 40 cikin 100 na maza da kashi 33 cikin 100 na mata ne kawai suke hakan.
Wasu na bahaya ƙasa da sau ɗaya a mako, wasu kuwa sau uku a rana. Bakiɗaya dai binciken ya nuna cewa ƙasa da rabin mutane ne ke bahaya yadda ya kamata, kuma matasa mata ne suka fi fuskantar kalubale.
Sai dai kuma ba wannan ne kaɗai gudunmawar da Heaton ya bayar a kimiyar bahaya ba. Ya taimaka wajen samar da wani sikeli mai suna The Bristol Stool Form Scale, wanda ake amfani dashi sosai wajen taimakawa likitoci gano masu matsala wajen narkewar abinci a ciki.
Sau nawa?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Hukumar lafiya ta NHS da wasu cibiyoyin lafiya sun bayyana cewa yin bahaya tsakanin sau uku a rana zuwa sau uku a mako shi ne daidai.
Sai dai 'daidai' da kuma 'mai lafiya' ba lallai abu ɗaya bane.
Masana kimiyya sun gano sau nawa muke bahaya, sai dai ba su yi komai ba domin amsa tambayar ko sau nawa yakamata muyi bahaya? Masu bincike na ƙara gano cewa yadda mutum ke bahaya wani babban alama ce na lafiyarsa.
A misali, wani bincike na 2023 ya binciki yanayin bahaya na manyan mutane 14,573 a Amurka. Adadin bahaya da aka fi samu shi ne sau bakwai a sati (kashi 50.7 na mutane), kuma yanayin bahayan da aka fi yi shi ne 'mai kama da maciji, mai santsi da laushi''.
Daga nan kuma masu binciken suka bibiyi mutanen na tsawon shekara biyar domin ganin ko akwai wata alaƙa tsakanin yawan yadda suke bahaya da mutuwa.
Sun gano cewa mutanen da ke bahaya mai laushi sau huɗu a sati na da kashi 1.78 na yiwuwar mutuwa cikin shekara biyar, fiye da waɗanda ke bahaya daidai sau bakwai a rana.

Asalin hoton, Emmanuel Lafont/ BBC
Tambayar ko bahaya sau nawa ne ya ke kasancewa mai kyau ya daɗe yana damun Sean Gibbons, wani masanin ilimin ƙwayoyin halitta a wata makaranta da ke Seattle a Amurka.
A shekarar 2024, Gibbon ya jagoranci wani bincike wanda ya rarraba manyan mutane masu lafiya su 1,400 zuwa kashi huɗu bisa la'akari da yadda suke bahaya; masu bahaya sau ɗaya ko biyu a mako, sai masu bahaya sau 3-6 a mako, sai masu bahaya sau 1-3 a rana, sai kuma masu gudawa.
Daga nan sai suka binciki ko akwai wani alaƙa tsakanin sau nawa mutum ke bahaya da ƙwayoyin halittar da ke cikin mutum. Daga nan sai ya binciki ko akwai alaƙa tsakanin yawan lokacin da aka bahaya da ƙwayoyin halittar da ke ciki.
Gibbon ya gano cewa masu bahaya akai-akai da ke bahaya sau ɗaya zuwa uku a rana na da adadi mafi yawa na ƙwayoyin halittar bacteria 'mai amfani' a cikinsu fiye da waɗanda basu fiye zuwa bayangida ba.
'' A cikin masu bahaya sau 3-6 a mako, mun ga ƙaruwar wasu ƙwayoyin halitta masu suna anaerobic microbes waɗanda ke samar da wani sinadari mai suna short chain fatty acids (SFA) in ji Gibbons. Ɗaya daga cikin waɗannan sinadari na SFA mai suna butyrate wanda aka sani da rage kumburi. Hakan na da muhimmanci saboda an gano cewa tsananin kumburi shi ne babban sanadiyyar kamuwa da cutuka kamar ciwon zuciya, nau'i na biyu na ciwon sukari da ma ciwon ƙwaƙwalwa na mantuwa''.
''Samun adadi mai yawa na sinadarin Butyrate na kuma taimaka maka sarrafa sukarin da ke jininka,'' in ji Gibbons.
Gibbons na ganin cewa dalili ɗaya da ya sa mutanen da ke bahaya sau ɗaya zuwa uku a mako suke da adadi mai yawa na sinadarai masu illa a cikin jininsu shi ne idan mutum ba ya bahaya sosai, bahayan na maƙalewa a cikinsa na lokaci mai tsawo.
Hakan na janyo ƙwayoyin halitta na Bacteria da ke ciki su cinye sinadaran da ke narka abinci su mayar da su SFA. Matsalar a nan ita ce, da zarar sinadaren narka abincin sun ƙare, ƙwayoyin bacteria za su fara canza sinadaran protein masu gina jiki - wanda hakan ke sakin sinadarai masu illa zuwa magudanar jini.
Waɗanannan sinadaren an san su wajen lalata sassan jiki kamar ƙoda da kuma zuciya.
A misali, ɗaya daga cikin sinadaran wanda ake kira phenylacetylglutamine, ya na taimakawa wajen kamuwa da ciwon zuciya.
Gibbons ya ce duk da dai bincike ya nuna cewa tsakanin bahaya sau uku a rana zuwa sau uku a sati shi ne daidai, binciken shi ya nuna cewa ko a rukunin masu bahaya sau 3-6 duk mako, akwai ƙaruwar sinadarai masu illa a magudanar jini.

Asalin hoton, Emmanuel Lafont/ BBC
Sai dai, kamar kullun, alaƙa ba ya nufin sanadi. Akwai yiwuwar cewa mutane da dama basu da cikakkiyar lafiya, ba za su iya bahaya sosai ba.
Yanayi ɗaya da za ka gane lafiyar cikinka shi ne tsawon lokacin da abinci ke tafiya a cikin cikinka. Za ka iya gwada hakan a gida cikin sauƙi ta hanyar cin abinci mai launi mai haske kamar masara, sai ka auna tsawon lokacin da zai ɗauka kafin ya fito.
A taƙaice, iya tsawo lokacin da abinci ke tafiya a cikin mutum, iya yiwuwar wahalar yin bahaya.
A shekarar 2020, masu bincike a makarantar Kings College da ke Landan sun bai wa mutane 863 kek mai launin shuɗi domin gwada tsawon lokacin da abinci ke tafiya a cikinsu.
Wannan wani ɓangare ne na binciken da ake yi domin gano yadda bambanci tsakanin ƙwayoyin halitta, da ƙwayoyin halittan da ke ciki, da wasu abubuwan ke tasiri kan yadda abinci daban daban ke shafar sukarin da ke jini da yanayin kitsen da ke jiki.
Binciken ya nuna cewa tsawon lokacin da abinci ke tafiya a ciki ya bambanta daga mutum zuwa mutum, wanda ya fara daga ƙasa da sa'oi 12 zuwa kwanaki.
Abin mamaki shi ne ƙwayoyin halittar da aka gani a cikin waɗanda suka fi yin bahaya yana da bambanci da waɗanda ba sa bahaya sosai, wanda aka gano masu bahaya sosai sun fi lafiyar ƙwayoyin halitta da ke ciki.
Kamar Gibbons, Emily Leeming, masaniyar kimiyyar ƙwayoyin halittar jikin ɗanadam a makarantar Kings College da ke Landan, ta na ganin cewa a cikin waɗanda bahaya ke daɗewa a cikinsu, ƙwayoyin halittar ba su samun sabon abinci- don haka sai su koma cin sinadaren da ke taimakawa wajen narkar da abinci, zuwa sinadaren carbohydrates zuwa sinadaren Protein masu gina jiki.
Hakan kuma na samar da wani abu da ke da illa ga lafiya.
Baya ga samun ƙwayoyin halittu na ciki masu lafiya, binciken Leeming ya kuma bayyana cewa masu gajeren lokaci da abinci ke tafiya a cikin su, wato masu bahaya akai-akai suna samun adadi mara yawa na kitsen tumbi.
Kitsen tumbin na da illa saboda yana kai wa ga kamuwa da cutuka kamar ciwon zuciya, ciwon sukari da wasu nau'i na ciwon daji.
A ƙarshe kuma, masu gajeren lokaci wajen tafiyar abinci a cikinsu na na adadi mara yawa na sukari da maiƙo a jininsu bayan sun ci abinci, wanda ke rage yiwuwar su na kamuwa da ciwon zuciya.
Sakamakon wannan binciken ya yi dai dai da abinda masana kimiyya suka sani game da masu wahalar yin bahaya da alaƙar hakan da ciwuka masu tsanani. Idan mutum na fama wurin yin bahaya, yana da barazana mafi girma na kamuwa da ciwon kansa na hanji.

Asalin hoton, Emmanuel Lafont/ BBC
Me bahayar ka ke cewa game da kai
Ba wai ga adadin bahayar da kake yi a duk mako ba - wanda zai iya bambanta tsakanin mutane, Leeming ta ce abin lura a nan shi ne ko akwai wani sauyi da aka kasa fahimta game da yadda aka saba yin bahaya.
Ta kuma bayar da shawarar cewa abu ne mai kyau ka rika bibiyar yadda ka ke bahaya domin ka san abin da ya ke daidai a wajen ka.
''Ya kamata duk mu rika kallon bahayarmu, saboda kamar wani gwaji ne na lafiyar ciki kyauta, ''inji Leeming. '' Ba wai kawai sau nawa ka yi ba, har da launi da kuma siffarsa. Abin da ka ke so ka gani shi ne bahaya mai tsayi da ke ɗan tsagi a jiki ko kuma mai santsi ba wani tsagi.''
Game da launi kuwa, idan ka ga wani launin baƙi ko ja a cikin bahaya, hakan na nuna alamar jini. Duk da dai mai yiwuwa akwai dalilin hakan mara hatsari, zai kuma iya kasancewa alama ce ta ciwon kansa na hanji, don haka yanada muhimmanci ka ziyarci likita cikin gaggawa.
Akwai kuma buƙatar ta tuntuɓi likitanka idan kana yawan yin gudawa ko kana saurin yin bahaya ko kana ciwon ciki sosai, ko kuma kumburin ciki.
Daga ƙarshe, idan kana so ka riƙa zuwa yin bahaya 'akai-akai', akwai matakai uku masu sauƙi da za ka yi. '' A binciken mu, mutanen da ke rukunin masu bahaya akai-akai suna cin ƴaƴan itatuwa da ganyayyaki sosai, suna shan ruwa sosai, kuma sunfi sauran motsa jikinsu,'' in ji Gibbons.










