Real za ta yi wasa uku cikin kwana bakwai a Santiago Bernabeu

Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Real Madrid za ta yi wasa uku cikin kwana bakwai da ya haɗa da Copa del Rey da La Liga da kuma Champions League a Santiago Bernabeu.

Ranar Alhamis Real za ta fara da karɓar bakuncin Celta a Copa del Rey zagayen ƴan 16, karon farko da za ta yi wasa a gida a 2025.

Ƙungiyar ta Bernabeu ta kawo wannan matakin bayan da ta yi waje da Deportiva Minera a zagayen ƙungiyoyi 32.

Kwana uku tsakani Real za ta yi wasa na biyu cikin kwana bakwai a gida a gasar La Liga, inda za ta kece raini da Las Palmas.

Real Madrid da Las Palmas sun tashi 1-1 a wasan farko a babbar gasar tamaula ta Sifaniya ta bana ranar Alhamis 29 ga watan Agustan 2024.

Daga nan Real za ta yi wasa na uku a gida a Champions League da Red Bull Salzburg ranar Laraba 22 ga watan Janairu.

Wasa uku da Real Madrid za ta fafata cikin kwana bakwai a gida:

  • Real Madrid da Celta ranar Alhamis 16 ga watan Janairu
  • Real Madrid da Las Palmas ranar Lahadi 19 ga watan Janairu
  • Real Madrid da Salzburg ranar Laraba 22 ga watan Janairu

Ranar Lahadi Real Madrid ta yi rashin nasara a hannun Barcelona da ci 5-2 a Spanish Super Cup da suka kara a Saudi Arabia.

Karo na biyu da Barcelona ta doke Real Madrid a kakar nan, bayan 4-0 a cikin watan Oktoba a gasar La Liga.

Barcelona ce kan gaba a yawan lashe Spanish Super Cup mai 15 jimilla, sai Real Madrid mai 13 a tarihi.