Jihohi shida da za su tantance wanda zai lashe zaɓen shugaban Amurka a 2024

    • Marubuci, James FitzGerald
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 6

Akwai kimanin mutum miliyan 240 da za su kaɗa ƙuri'a a zaɓen Amurka na wannan shekara, to sai dai mutane ƙalilan ne za su tantance wanda zai zama shugaban Amurka na gaba.

Masana sun ce akwai wasu muhimman jihohi marasa tabbas ga duka 'yan takarar biyu, Kamala Harris ta Democratic da kuma Donad Trump na Republican

Jihohi ne guda shida - Arizona da Georgia da Michigan da Nevada da Pennsylvania da kuma Wisconsin - waɗanda inda ɗan takara ya cinye su to la-shakka zai lashe zaɓen shugaban ƙasar.

Don haka ne duka jam'iyyun biyu ke ƙoƙarin yaƙin neman zaɓe a waɗanan jihohi, domin samun ƙuri'unsu.

Arizona

Mista Biden ya samu nasarar zama shugaban Amurka ne a 2020 bayan samun goyon bayan jihar, wadda ta zaɓi ɗan takarar Democratic karon farko tun shekaraun 1990.

Jihar ta yi iyaka da ƙasar Mexico, kuma ta zama jihar da aka fi muhawara a kanta kan batun baƙin haure.

Yawan mutanen da ke tsallakawa ta kan iyakar a 'yan watannin baya-bayan nan ya ragu, wani batu da ke jan hankalin masu zaɓe a jihar.

Mista Trump ya sha sukar Kamala Harris, kan batun 'yan ci-rani, saboda Mista Biden ya dora mata laifin gaza magance rikicin kan iyakokin ƙasar.

Ya sha alawashin gudanar da gagarumin 'korar baƙi'' a tarihin Amurka idan ya sake zama shgaban kasar.

Haka kuma jihar Arizona na fama da rikicin 'yancin zubar da ciki, bayan da jam'iyyar Repubican ta yi yunƙurin sake kakaba dokar haramta zubar da ciki ko ta wace hanya ce a jihar.

Batun zubar da ciki lamari ne da ya ja hankalin Amurka tun 2022, lokacin da kotun ƙolin Amurka da soke dokar da ta bai wa mata 'yancin zubar da ciki.

Georgia

Jihar Georgia na cikin wannan rukuni, inda a zaɓen 2020 Mista Biden ya doke Trump a jihar.

Zargin katsalandan a zaɓen jihar na daga cikin laifuka huɗu da aka zargi Donald Trump da aikatawa. An zarge shi, tare da wasu mutum 18 da hada baki don rage tazarar da Biden ya ba shi a jihar. To amma ya musanta aikata ba daidai ba, kuma akwai yiwuwar a saurari ƙarar kafin zaɓen ƙasar.

Georgia ce jihar da ta fi kowace jiha a Amurka yawan Amurkawa 'yan asalin Afirka inda take da kashi 33 cikin 100, kuma an yi amanna cewa hakan ne ya sa Biden ya lashe jihar a 2020.

Michigan

Jihar mai albarkar koguna, wanda ya lashe ta ya samu nasarar zama shugaban Amurka har sau biyu a baya-bayan nan. Duk da goyon bayan da jihar ta bai wa Biden a 2020, ta zama wadda ta riƙa nuna adawa da shi musamman kan goyon bayan da shugaban ya rika bai Isra’ila a yakin da take yi a Gaza.

A lokacin ƙuri'ar jin ra'ayin jama'ar da aka gudanar a jihar cikin watan Fabrairu, fiye da mutum 100,000 suka zaɓi “rashin amincewa” a kan ƙuri'arsu, bayan da aka samu kiraye-kiraye daga 'yan gwagwarmaya da ke son Amurka ta janye tallafin soji da take bai wa Isra'ila.

Abu ne sananne jihar ta fi kowace jiha yawan Amurkawa 'asalin Larabawa - adadin mutanen da ke goyon bayan Biden waɗanda yanzu suka sauya matsaya. To amma Ms Harris ta fara yaƙin neman zaɓenta da kausasan kalamai kan Isra'ila fiye da shi, inda wasu masu zaga-zangar neman a dakatar da yaki a Gaza, suka faɗa wa BBC cewa suna fatan za ta tausaya fiye da Biden.

Mista Trump ya bayyana muhimmancin jihar a hanyarsa ta samun nasarar zaɓen. Yayin da yake magana kan Gabas ta Tsakiya, ya yi kira ga Isra'ila ta kawo ƙarshen ayyukanta kan Hamas a Gaza, to amma ''ta kawo ƙarshen cikin gaggawa''.

Nevada

Jihar Nevada da ake yi wa kirari da 'Zinariyar jiha' ta zaɓi jam'iyyar Democrat a zabuka da dama da suka gabata, to sai dai akwai yiwuwar a samu sauyi a bana.

Alƙaluman ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a na baya-bayan nan da kamfanin 538 ya gudanar sun nuna cewa Mista Trump na kan gaba da Biden da gagarumar tazara.

To sai dai 'yar takara irin Ms Harris mai goyon bayan matasa da sauran rukunin jama'a na iya rage tazarar.

Duka 'yan takarar na rige-rigen lashe jihar mai yawan Amurkawa 'yan asalin Latin.

Duk da cewa afili take an samu bunƙasar tattalin arziki da ƙaruwar ayyukan yi a Amurka, tun bayan da Mista Biden ya karɓi ragamar shugabancin ƙasar, an samu jinkirin warwarewar annobar Covid a jihar Nevada, fiye da kowace jiha.

Jihar ce ta fi kowace yawan marasa ayyukan yi, inda take da kashi 5.1 cikin 100, bayan jihar California da gundumar Columbia, kamar yadda alƙaluman baya-bayan nan da hukumar ƙididdigar ƙasar ta fitar.

Mista Trump ya alƙawarta cewa, idan ya samu nasara, zai maido da ajandar rage kudin haraji da wasu ƙa'idoji.

Pennsylvania

Pennsylvanians ta zama ta daban tsakanin jihohin ƙasar da ke jin raɗaɗin matsin tsadar rayuwa, sakamakon hauhawar farashin kayayyaki.

Farashin kayan masarufi ya yi tashin gwauron zaɓo a jhar fiye da sauran jihohin ƙasar, kamar yadda alƙaluman kasuwanci a ƙasar suka nuna.

A baya-bayan nan BBC ta bayar da rahoton yadda jama'a ke fama da tsadar raywa a gundumar Erie ta jihar, inda mutum guda cikin kowanne takwas ke fama da matsalar rashin abinci.

Jihar ta nuna muhimmancinta a za ben ƙasar a 2020, bayan da ta goyin bayan Biden, wanda ke da alaƙa mai ƙarfi da mutanen birnin Scranton, inda ya taso - waɗanda galibinsu ma'aikatan gwamnati.

Matsalar hauhawar farashi a faɗin Amurka ka iya shafar Ms Harris, yayin da masu zaɓe ke la'akari da hauhawar farashi wajen yanke shawarar wanda za su zaɓa.

Mista Trump ya ɗauki matakin ɗora wa Harris laifukan gazawar Biden a fannin tattalin arzikin ƙasar.

Wisconsin

Jihar Wisconsin- da ake yi wa kirari da 'kura' - ta kasance jihar da ta goyi bayan shugaban Amurka a zaɓukan 2016 da 2020, ta hanyar tazarar da ta zarta 20,000 a kowane lokaci.

Masu sharhi na ganin tazarar da ake samu a jihohi irin wannan, 'yan takarar ƙananan jam'iyyu ka iya yin tasiri a kan manyan 'yan takarar biyu.

Kuri'ar jin ra'ayin jama'a sun nuna cewa al'ummar jihar sun fi mara wa 'yan takarar indifenda baya irin su Robert f Kennedy Jr - wanda ke ƙoƙarin samun ƙuri'ar jihar da na wasu a sauran jihohin don rage wa Ms Harris da Trump yawan ƙuri'u.

Mista Trump ya ce jihar na da ''matuƙar muhimmanci .... idan muka lashe ta, to mun samu nasara''.

A binin Milwaukee na jihar ne dai za a gudanar da babban taron jam'iyyar Republican na lokacin bazara.

Ita ma Ms Harris ta zaɓe birnin Milwaukee a matsayin wurin da ta fara gangamin yaƙin neman zaɓen bayan zama 'yar takara.