Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lewandowski ne kan gaba a cin ƙwallaye a La Liga kawo yanzu
Robert Lewandowski ne kan gaba a yawan zura ƙwallaye a raga a La Liga, bayan wasa huɗu da fara La Liga ta 2024/25.
Ɗan wasan Poland mai taka leda a Barcelona ya ci huɗu a raga a dukkan karawa huɗun da ya buga da fara kakar nan.
Lewandowski ya fara cin ƙwallo biyu ranarr 17 ga watan Agusta a wasan da Barcelona ta je ta doke Valenci 2-1 a farkon fara babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Ya kuma ci Athletic Bilbao ɗaya a karawar da Barcelona ta yi nasara 2-1 a wasan mako na biyu ranar Asabar 24 ga watan Agusta.
Amma bai zura ƙwallo ba a ragar Rayo Vallecano a karawar mako na uku da Barcelona ta ci 2-1 ranar Talata 27 ga watan Agusta.
A wasan mako na huɗu ya samu cin Real Valladolid ƙwallo ɗaya a fafatawar mako na huɗu ranar Asabar 31 ga watan Agusta, inda Barcelona ta ɗura 7-0.
Haka kuma ɗan wasan Barcelona, Raphinha shi ne na biyu a jerin waɗanda ke kan gaba cin ƙwallaye mai uku a raga.
Ɗan wasan tawagar Brazil ya zura uku rigis a mako na huɗu a wasan da Barcelona ta sharara 7-0 a ragar Valladolid ranar Asabar 31 ga watan Agustan 2024.
Kawo yanzu Barcelona, wadda ta ci ƙwallo 13 tana ta ɗaya a kan teburi da maki 12, ita kaɗai ce ta lashe dukkan wasa huɗu da fara kakar nan.
Real Madrid da Atletico Madrid da Villareal sune ke biye da Baarcelona, kowacce tana da maki takwas, bayan karawa huɗu.
Jerin waɗanda ke kan gaba a yawan cin ƙwallaye a La Liga
- Lewandowski Barcelona 4
- Raphinha Barcelona 3
- Mbappé Real Madrid 2
- Sancet Athletic Club 2
- Duro Valencia 2
- Martínez Deportivo Alaves 2
- Aspas Celta Vigo 2
- Iglesias Celta Vigo 2
- Mingueza Celta Vigo 2
- Llorente Atletico 2
Wasannin mako na biyar a La Liga
Ranar Juma'a 13 ga watan Satumba
- Real Betis da Leganes
Ranar Asabar 14 ga wwatan Agusta
- Mallorca da Villarreal
- Espanyol da Deportivo Alaves
- Sevilla da Getafe
- Real Sociedad da Real Madrid
Ranar Lahadi 15 ga watan Satumba
- Celta Vigo da Real Valladolid
- Girona da Barcelona
- Las Palmas da Athletic Club
- Atletico Madrid da Valencia