Chelsea za ta shiga zawarcin Sancho, Liverpool ta ƙara ƙaimi kan Mamardashvili

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Chelsea za ta yi tayin ba zata kan ɗan wasan gaban Manchester United da Ingila mai shekara 24, Jadon Sancho, 24. (Athletic - subscription required)

Liverpool ta gabatar da tayin £34m kan mai tsaron gidan Valencia da Georgia mai shekara 23, Giorgi Mamardashvili. (Relevo - in Spanish)

Paris St-Germain ta gabatar wa Manchester United damar ɗaukar ɗan wasan tsakiyarta, ɗan ƙasar Uruguay mai shekara 23, Manuel Ugarte, a matsayin aro na tsawon kakar wasan bana. (Telegraph - subscription required)

Manchester City na kan gaba wajen neman sake ɗaukar tsohon ɗan wasan tsakiyar Jamus, Ilkay Gundogan daga Barcelona, bayan rahotanni sun nuna cewa ɗan wasan mai shekara 33 ya fi ƙaunar komawa taka leda a gasar firimiya. (Athletic - subscription required)

Barcelona ta janye daga zawarcin ɗan wasan bayan Manchester City da Portugal mai shekara 30, Joao Cancelo, saboda ba ta amince da biyan sa albashin £12m ba. (Sport - in Spanish)

Manchester United ta amince da sakin ɗan wasan ta ɗan asalin Uruguay mai shekara 22, Facundo Pellistri, wanda zai koma Panathinaikos ta Girka. (Telegraph - subscription required)

Burnley na sha’awar ɗaukar ɗan wasan tsakiyar Manchester United da Tunisia, Hannibal Mejbri, mai shekara 21. (Athletic - subscription required)

Bayer Leverkusen ta tuntuɓi Liverpool game da shirin ta na sayen Sepp van den Berg, wanda ake sa ran Liverpool na neman £25m kan ɗan wasan bayan. (Florian Plettenberg)

Manchester United ta shirya sayar da ɗan wasan tsakiyar Scotland mai shekara 27, Scott McTominay, ga Napoli, domin cika ƙa’idar kashe kuɗi da hukumomi suka sanya. (Corriere dello Sport - in Italian)

Barcelona na ƙoƙarin ɗaukar ɗan wasan gaban AC Milan da Portugal, Rafael Leao kafin ƙarshen kasuwar cinikin ƴan wasa. (Mundo Deportivo - in Spanish)