Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Morecambe ta ɗauki aron Williams daga Liverpool
Morecambe ta ɗauki aron mai tsaron bayan Liverpool, Rhys Williams da zai taka mata leda zuwa watan Janairun 2025.
Tsohon dan wasan tawagar Ingila ta matasa ƴan kasa da shekara 21 ya buga wasa tara a Premier League a ƙungiyar Anfield.
Mai shekara 23 ya je wasannin aro a Aberdeen da Port Valea a bara daga baya ya koma Liverpool, wanda ya sha fama da jinya.
Rhys Williams ya buga wasa 19 a Liverpool, wanda rabon da ya taka mata leda tun Mayun 2021.
Shi ne na 18 da zai buga League Two a bana.
Ƙungiyar da Derek Adam ke jan ragama ta yi rashin nasara a wasa biyu a jere da fara kakar bana, za su ziyarci Doncaster Rovers ranar Asabar.