Ko Trump zai iya yin wa'adi na uku a matsayin shugaban Amurka?

Asalin hoton, EPA
- Marubuci, Graeme Baker
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
Donald Trump ya ce "ba da wasa yake yi ba" kan aniyarsa na son yin wa'adin mulki karo na uku a matsayin shugaban Amurka.
Kundin tsarin mulkin Amurka ya ce "babu wani mutum... da za a iya zaɓa fiye da sau biyu", amma wasu magoya bayan Trump sun ce za a iya samun wasu hanyoyi na daban.
Shin Trump na son wa'adin mulki na uku?
Da aka tambaye shi a wata tattaunawa da gidan talabijin na NBC a ƙasar kan yiwuwar neman takara karo na uku, Trump ya ce "akwai hanyoyi da za ka iya yin haka".
"Ba da wasa nake yi ba... mutane da yawa na son na sake tsayawa takara," in ji shi. "Sai dai, ina faɗa musu cewa akwai doguwar hanya, kuma ya yi wuri mu nuna buƙatar haka ganin yanzu muka fara gwamnati."
An tambayi Trump, wanda zai cika shekara 82 lokacin da zai kammala wa'adin mulkinsa na biyu cewa, ko yana son ci gaba da mulkin ƙasar wanda shi ne abu mafi wahala.
"Eh, ina son yin aiki," in ji shi.
Waɗannan ba su ne kalamansa na farko ba kan batun. A watan Janairu, ya faɗa wa magoya bayansa cewa zai zama "babbar dama a rayuwarsa mulki ba sau ɗaya ba, amma sau biyu ko uku ko ma huɗu". Sai dai, a lokacin ya ce da wasa yake yi.
Me kundin mulkin Amurka ya ce?
Dangane da batun, kundin tsarin mulkin Amurka ya haramtawa kowane mutum neman takara sau uku. Kundin mulkin na 22 da aka yi garambawul ya bayyana cewa:
"Babu wani mutum da za a zaɓa zuwa ofishin shugaban ƙasa fiye da sau biyi, kuma babu wani mutum da ya taɓa riƙe ofishin shugaban ƙasa, ko matsayin shugaban ƙasa sama da wa'adin shekara biyu na wani da aka zaɓa shugaban ƙasa, da za a iya zaɓa a kujerar shugaban ƙasa fiye da sau ɗaya."
Sauya kundin mulkin na buƙatar amincewar kashi biyu bisa uku na ƴan majalisa a majalisar dattijai da kuma ta wakilai a ƙasar, da kuma amincewar kashi uku bisa huɗu na gwamnatocin jihohi a ƙasar.
Jam'iyyar Republican ta Trump ita ke iko a dukkan majalisun ƙasar - sai dai ba ta rinjayen da ake buƙata. Ƙari kuma shi ne, jam'iyyar Democrat na iko da ƴan majalisa 18 cikin 50 a majalisun dokokin jihohi a Amurka.
Ta yaya Trump zai zama shugaban ƙasa karo na uku?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Magoya bayan Trump sun ce kundin mulkin na cike da kura-kurai, kuma kotu ba ta hakan daidai ne ko akasin haka.
Sun kalubalanci cewa kundin mulki na 22 da aka yi wa garambawul kawai ya haramtawa mutum ne "zaɓarsa fiye da sau biyu a mukamin shugaban ƙasa - amma bai ce komai ba kan wanda ya gaji mulki.
Karkashin wannan, Trump zai iya zama ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa ga wane ɗan takara - watakila ya kasance ga mataimakinsa na yanzu, JD Vance - a zaɓen 2028.
Idan suka ci zaɓe, za a rantsar da ɗan takarar zuwa fadar White House kuma nan take sai ya yi murabus - abin da zai sa Trump ya gaji mulkin.
Steve Bannon, wani tsohon mai ba da shawara ga Trump, ya ce ya yi imanin cewa Trump zai "yi takara kuma zai samu nasara", inda ya ƙara da cewa "akwai wasu hanyoyi na daban" yadda Trump zai yi mulki sau uku.
Andy Ogles, ɗan majalisar wakilai daga jihar Tennessee kuma ɗan jam'iyyar Republican, ya ba da wata shawara a watan Janairu - inda ya yi kira don yi wa kundin mulkin ƙasar garambawul domin bai wa shugaban ƙasa damar yin mulki har sau uku - muddin ba a jere ba ne.
Hakan na nufin cewa Trump kaɗai cikin dukkanin tsofaffin shugaban Amurka da ke raye da zai samu wannan dama - Barack Obama da Bill Clinton da George W Bush dukkansu sun yi wa'adin mulki biyu ne a jere, yayin da Trump ya lashe zaɓe a 2016, ya faɗi a 2020 - sannan ya sake yin nasara a 2024.
Su wa ke adawa da Trump kan mulki sau uku?
Ƴan jam'iyyar Democrat sun yi kaƙkausar suka da kuma nuna adawa da matakin.
"Wannan abin Alla-wadai ne da kuma ƙoƙarinsa na karɓe iko da gwamnati da watsi da dimokraɗiyya," a cewar Daniel Goldman, ɗan majalisar birnin New York wanda ya jagoranci alkalai lokacin da aka tsige Trump karon farko, bisa wasu laifuka guda biyu.
"Idan ƴan jam'iyyar Republican suka amince da kundin mulki, za su yi adawa da yunkurin Trump na neman wa'adin mulki karo na uku."
Wasu a cikin jam'iyyar Trump ma na ganin abin bai dace ba.
Ɗan majalisar dattijai na jam'iyyar Republican Sanata Markwayne Mullin daga jihar Oklahoma, ya faɗa a watan Fabrairu cewa ba zai goyi bayan yunkurin sake zaɓar Trump karo na uku ba.
"Ba zan sauya kundin mulki ba, sai dai in Amurkawa ne suka buƙaci hakan," kamar yadda Mullin ya faɗa wa gidan talabijin na NBC.
Me masana shari'a suka ce?
Derek Muller, wani Farfesa a jami'ar Notre Dame, ya ce kundin mulki na 12 da aka yi wa garambawul ya bayyana cewa "babu wani da ba shi da damar yin takarar kujerar shugaban ƙasa da zai iya yin takarar kujerar mataimakin shugaban ƙasa a Amurka".
Wannan na nufin cewa mutumin da ya yi mulki sau biyu a matsayin shugaban ƙasa - ba shi da damar yin takarar kujerar mataimakin shugaban ƙasa, a fahimtarsa.
"Babu wata hanya da nake ganin za a bi wajen takarar shugaban ƙasa fiye da sau biyu," in ji shi.
Jeremy Paul, wani Farfesa a jami'ar Boston, ya faɗa wa kafar yaɗa labarai ta CBS cewa "babu wan bayani kwakkawara kan a ɓangaren shari'a" na yin mulki sau uku.
Akwai wanda ya yi mulki fiye da sau biyu?

Asalin hoton, Getty Images
An zaɓi Franklin Delano Roosevelt har sau huɗu, a watan Afrilun 1945.
Yaƙin Duniya II ya dabaibaye wa'adin mulkin Roosevelt - kuma ana yawan bayyana faruwar shi kan tsawaita wa'adin mulkinsa.
A lokacin, ba a rubuta batun yin wa'adin mulki sau biyu a kundin mulkin Amurka ba - abu ne da aka fara yi tun bayan lokacin da George Washington ya ki buƙatar yin mulki sau uku a 1796.
Tsawaita wa'adin mulkin Roosevelt ya janyo abin ya zama doka a kundin mulki na 22 da aka yi wa garambawul a farkon shekarun 1950.












