Newcastle na zawarcin Scalvini, Arteta ya sa wa'adin ƙulla yarjejeniya da Gyokeres

Asalin hoton, Getty Images
Newcastle United tana zawarcin ɗanwasan Italiya Giorgio Scalvini yayin da ƙungiyar ke fatan ɗaukan ɗanwasan na Atalanta mai shekara 21 kan kusan fam miliyan 30. (Times - subscription required)
Kocin Arsenal Mikel Arteta ya sa wa'adin ƙasa da mako biyu ga ƙungiyar ta cimma yarjejeniya kan ɗanwasan Sporting Viktor Gyokeres mai shekara 27 yayin da ɗanwasan RB Leipzig mai shekara 22 Benjamin Sesko da Ollie Watkins mai shekara 29 da ke buga wa Aston Villa suka kasance cikin jerin ƴanwasan da ake zawarci. (Mirror)
Barcelona za ta sake tunkarar ɗanwasan Liverpool mai shekara 28 Luis Diaz bayan da Nico Williams ɗan asalin Sifaniya mai shekara 22 ya sabunta kwantiraginsa da Athletic Bilbao. (Fabrizio Romano)
Ɗanwasan Everton mai shekara 35 Idrissa Gueye wanda kwantiraginsa ya ƙare a ranar Litinin ya ƙulla sabon kwantiragin shekara guda da zaɓin ƙarin shekara guda. (Footmercato - in French)
Tottenham na cikin ƙungiyoyin da ke nuna sha'awar sayen ɗanwasan Genoa Koni de Winter mai shekara 23 yayin da kulob ɗinsa na Italiya ya yi masa farashin fam miliyan 21.5. (Talksport)
Napoli na duba yiwuwar yin gogayya da Manchester United da Al Qadsiah ta Saudiyya a zawarcin ɗanwasan a Fiorentin mai shekara 25 Moise Kean. (Calciomercato - in Italian)
Burnley da Crystal Palace na daga cikin ƙungiyoyin Firimiya da ke sha'awar sayen ɗanwasan Napoli mai shekara 25 Jens Cajuste wanda ya shafe kakar da ta gabata yana zaman aro a Ipswich Town. (Sky Sports)
Crystal Palace ta kuma yi tayin sayen ɗanwasan Ajax Borna Sosa yayin da ɗanwasan mai shekara 27 da ke buga wa Croatia ya kasance cikin jerin zaɓin da ɓangaren Oliver Glasner ke duba yiwuwar ɗauka. (Athletic - subscription required)
Inter Miami na ci gaba da tattaunawa da ɗanwasan Argentina Lionel Messi mai shekara 38 kan tsawaita kwantiraginsa da zai ƙare a ƙarshen bana. (ESPN)















