Van Dijk: Ban san makomata ba idan Klopp ya bar Liverpool

Asalin hoton, Getty Images
Kyaftin din Liverpool, Virgil van Dijk ya ce ba shi da tabbas ko zai ci gaba da taka leda a Liverpool, idan Jurgen Klopp ya bar kungiyar a karshen kakar nan.
A makon jiya ne Klopp ya sanar da cewar zai bar Liverpool a karshen kakar bana.
Klopp ne ya sayo Van Dijk kan fam miliyan 75 a Janairun 2018 daga Southampton, wanda yake da kwantiragi da Liverpool zuwa karshen kakar 2025.
An tambaye shi ko zai ci gaba da taka leda a Liverpool, bayan Klopp ya ajiye aikin? Sai Van Dijk ya ce, ''Wannan babbar tambaya ce. Amma ba ni da amsa.''
Mataimakin koci, Pepijn Lijnders da Peter Krawietz da kuma Vitor Matos duk za su bar Liverpool tare da Klopp.
Haka kuma kwantiragin dan kwallon Masar, Mohamed Salah da mai tsaron bayan Ingila, Trent Alexander-Arnold za su kare a karshen kakar 2025 a Liverpool.
''Akwai jan aiki a gaban Liverpool, abin da na sani kenan,'' in ji Van Dijk,
''Wajen maye gurbin masu horarwa baki daya da wasu abubuwan da suke bukatar sauyi.''
Liverpool na takarar kofi hudu a kakar nan, wadda take cikin Kofin FA Cup, ita ce ta daya a Gasar Premier kuma ta kai wasan karshe a Kofin Carabao.
Haka kuma kungiyar ta Anfield ta kai zagaye na biyu a gasar Zakarun Turai ta Europa League.










