Yadda za ka gano ko kana da kansar hanji

Mace a bandaki

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ka gaggauta zuwa asibiti da ka ji wani abu ba daidai ba a jikinka
An wallafa

Dame Deborah James, wadda ta rasu a sakamakon kamuwa da cutar daji ta hanji tana shekara 40, ta bayar da shawara ga kowa, da mutum ya rika duba kashinsa a matsayin wata hanya ta fadakarwa a kan wannan nau'in cutar kansa.

Mun amsa tambayoyin da yawancin mutane ke yi game da wannan nau'in cutar daji da kusan galibin mutane ke gamuwa da ita a Birtaniya.

Ta yaya zan gane alamun cutar?

Akwai muhimman abubuwa uku da za ka duba:

  • Ka ga jini a kashinka ba tare da wani dalili ba - zai iya kasancewa mai haske-haske ko kuma mai duhu.
  • Sauyin yadda kake kashi - kamar yawan zuwa bahaya ko kashinka ya zama da tauri ko ruwa-ruwa.
  • kasan cikinka ya rika ciwo ko kuma kunburin ciki, ka rika jin cikin bam-bam.

Za a iya samun wasu karin alamun:

  • Ramewa
  • ka yi kashi ka ji kamar da saura a cikinka
  • jin gajiya ko juwa ko hajijiya fiye da yadda ya kamata

Ganin wadannan alamomi ba wai lalle hakan na nufin kana da cutar daji ta hanji ba ne.

Amma shawara ita ce ta je ka ga likita, idan har ka ga alamar ta wuce mako uku ko fi, ko kuma idan ba ka jin dadi.

Hakan na nufin za a iya saurin gano matsalar a magance ta.

Ita cutar daji gano ta da wuri kan sa a iya magance ta da wurwuri.

Wani lokaci cutar daji na iya hana mutum bahaya, wanda hakan na iya toshe dubura.

Wannan na iya sa ciwon ciki mai tsanani da rashin yin kashi da kuma rashin lafiya.

Idan ka samu kanka a wannan yanayi to ba shakka kana bukatar ka garzaya zuwa asibiti da gaggawa.

Ta yaya zan iya duba kashina?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ka sa ido sosai ka ga yadda kashinka yake kuma kar fa ka ji kunyar yin magana a kai.

Ka duba sosai ka ga ko akwai jini a cikin kashinka ko kuma daga can kasan kasin.

Jini mai haske ka iya kasancewa daga wata jijiya ce da ta kunbura a duburarka wato basir kenan, haka kuma zai iay kasancewa cutar dajin ce ta janyo.

Idan jinin yana da duhu a kashinka, to hakan zai iya kasancewa daga hanjinka ko kuma tumbinka yake, shi ma kuma zai iya kasancewa abin damuwa.

Za kuma ka iya samun sauyi a yanayin bahayarka, kamar kashin ya kasance ruwa-ruwa ko kuma zuwa bandaki fiye da kima.

Ko kuma ka ji kamar da sauran kashi a cikinka bayan ka je bandaki.

Haka kuma rashin zuwa bandaki yadda ya kamata.

Kungiyar likitocin cutar kansar hanji ta Birtaniya na bayar da shawar a rika rubuta jerin bayanan alamun da mutum ya gani kafin ya je ganin likita, saboda kada ka manta da wani abin.

Likitoci sun saba ganin mutane da alamun matsaloli daban-daban na hanji, saboda haka ka gaya wa likita duk wani sauyi da ka gani ko kuma jinin da ka gani domin a gano abin da ya haifar da hakan.

Auduga da jini

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ka duba jini a kashinka ko kuma a duburarka

Me ke janyo cutar kansa ta hanji?

Ba wanda zai iya cewa takamaimai ga abin da ke janyo cutar, to amma akwai abubuwan da ake ganin za su iya janyo ta:

  • yawan shekarunka - yayin da kake shekaru kana shiga yanayin da za ka iya kamuwa da cutar daji - yawancin masu wannan cuta ta kansa ta hanji manya ne 'yan sama da shekara 50
  • Cin abinci da jan nama mai yawa da kuma abincin gwan-gwani (na kamfani wanda ake sayar wa a kanti)
  • shan taba kan iya kara hadarin kamuwa da cutar daji
  • shan giya da yawa
  • teba da yawa
  • idan kana da matsalar da hanjinka ke hayayyafar wasu 'yan kananan kumburi ko kuraje, da ka iya zama daji

Ko ana gadon cutar dajin ta hanji?

Yawanci ba a gadon cutar, to amma idan akwai wani a danginku da aka taba samu da ita kafin ya kai shekara 50 to yana da kyau ka gaya wa likita.

Akwai yanayi na gado kamar matsalar kuraje ko kumburi a hanji, wanda hakan ka iya haddasa cutar. To amma likitoci za su iya magance wannan idan sun san da ita.

Hoton cikin mutum

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kansar hanji za ta iya farawa tun daga babban hanji ko kuma saman dubura

Yadda za ka kare kanka daga hadarin cutar?

Masana kimiyya sun ce za a iya kare kusan rabin hadarin kamuwa da cutar idan mutum yana bin hanyoyin rayuwa na lafiya.

Wannan na nufin yawan motsa jiki da cin 'ya'yan itace da ganyayyaki da rage cin maiko da shan ruwa kusan kofi shida zuwa takwas a duk rana.

Bayan wadanna akwai kuma bukatar zuwa ganin likita a duk lokacin da ka ga wata alama, da kuma amfani da damar yin gwajin cutar daji a duk lokacin da aka samu damar.

Mutum na ciwon ciki

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ciwo da kumburin ciki - idan kana jin cikinka cike kuma ya dame, wannan ka iya zama wata alama da cutar dajin hanji

Za a iya min gwaji?

Ana yin gwaji don gano alamun cutar daji ta hanji tun ba ta yi girma ba.

Akwai kayan gwaji na gida, wanda ke gano awata lamar jini a kashinka. Gwajin da za ka iya yi a gida ka aika asibiti.

Sai dai ba kowa ba ne yake samun wannan abin gwaji, sai wadanda ke rukunin shekarun da ake ganin za su iya samun cutar.

Ana yin gwajin a fadin Birtaniya.

  • A Ingila a hankali ana rage yawan shekarun da mutum ya cancanta a yi masa gwajin daga 60 zuwa 50 zuwa sama.

Ba a samun dacewa dari bisa dari a bincike, wanda kuma zai iya kaiwa ga yin maganin da zai iya cutarwa ko kuma wanda bai kamata ba, idan ana gwajin mutane da yawa masu lafiya.

Saboda haka idan kai matashi ne kuma kana da alamun cutar, yana da kyau ka san alamun kuma ka ziyarci likitanka idan har ka damu - kada ka sayi kayan gwajin ka je ka yi da kanka, saboda sakamakon ka iya ba ka wani abu mai rikitarwa.

kayan gwajin cutar a gida

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Hukumar lafiya a Birtaniya tana aika wa mutanen da shekarunsu ke rukunin wadanda ke kamuwa da cutar, kayan gwaji har gida domin gano ta da wuri

Yaya ake gano cutar kansa ta hanji?

Da zaran da mayar da kayan gwajin da ka yi, za a sanar da kai idan ba ka dauke da cutar ko kuma asibitinka ya tuntube ka domin a yi maka karin gwaje-gwaje.

Karin gwajin ka iya kasancewa wanda za a sanya maka wata 'yar karamar na'urar daukar hoto a cikinta wadda za ta ratsa cikin hanjinka - ko kuma daukar hoton wani gefe na hanjin.

Sama da kashi 90 cikin dari na mutanen da aka gano suna dauke da cutar tun tana farko-farkonta suna iya ci gaba da rayuwa karin tsawon shekara biyar ko fi, sabanin kashi 44 cikin dari na wadanda aka gano cutar bayan da ta yi nisa.

Damar rayuwa ga wadanda aka gano suna dauke da cutar a Birtaniya ta ninka sama da kashi biyu a shekara 40 da ta gabata.

Sama da rabin masu cutar yanzu suna rayuwa tsawon shekara 10 ko fi sabanin yadda ake gani a shekarun 1970.

Wannan cuta kamar sauran cutar daji, mutanen da ke rukunin shekara 15 zuwa 40 suna da damar rayuwa sosai, saboda cutar daji ta fi kamawa da kuma illa ga tsofaffi ko masu yawan shekaru.

Wadanne hanyoyin magani ake da su yanzu?

Ana maganin cutar daji ta hanji musamman ma idan ana gano ta da wuri.

A duk matakin da aka gano mutum na dauke da cutar za a iya gaya masa abin da za a iya yi a kai.

Wannan ka iya kasancewa tiyata ko gashi ko kuma amfani da magunguna domin kashe kwayoyin cutar, ya dai danganta ga yanayin cutar a jikin mutum.

Wadanne matakai ake da su na girman cutar?

  • Mataki na 1 - cutar karama ce kuma ba ta yadu ba
  • Mataki na 2 - cutar ta yi girma, amma har yanzu ba ta fara yaduwa ba
  • Mataki na 3 - ta fara yaduwa a jikin wasu jijiyoyin da ke kusa da ita
  • Mataki na 4 - cutar ta yadu har ta kama wani bangare na ciki ta haihu