Liverpool ta san makomarta a gasar Europa

Asalin hoton, Getty Images
An wallafa
An fitar da jadawalin gasar Europa wanda za a soma kece raini daga ranar 21 ga watan Satumbar bana.
Brighton na rukunin guda da Ajax da Marseille da kuma AEK Athens a zagayen farko na gasar Europa.
A yayin da ita kuma Liverpool za ta hadu da LASK, Union St-Gilloise da kuma Toulouse .
Ita kuwa West Ham za ta kara ne da Olympiacos, Freiburg da kuma TSC Backa Topola.
Ga cikakken jerin wasannin zagayen farko na gasar:
- Rukunin A: West Ham, Olympiacos, Freiburg, TSC Backa Topola
- Rukunin B: Ajax, Marseille, Brighton, AEK Athens
- Rukunin C: Rangers, Real Betis, Sparta Prague, Aris Limassol
- Rukunin D: Atalanta, Sporting Lisbon, Sturm Graz, Rakow
- Rukunin E: Liverpool, LASK, Union St-Gilloise, Toulouse
- Rukunin F: Villarreal, Rennes, Maccabi Haifa, Panathinaikos
- Rukunin G: Roma, Slavia Prague, Sheriff Tiraspol, Servette
- Rukunin H: Bayer Leverkusen, Qarabag, Molde, BK Hacken







