Lafiya Zinariya: Abubuwan da za ki buƙata wajen yin ƙunzugun da ake ɗinkawa
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1
Koyon ɗinka ƙunzugun da ake yi da tufafi domin koyar da wasu mata ko rabawa kyauta na daga cikin hanyoyin da ake bi domin yaƙi da rashin samun abin tare jinin haila da miliyoyin mata ke fuskanta a sassan duniya daban-daban.
A Najeriya kamar wasu ƙasashe wasu mata sun yunƙuru wajen koyar da yadda ake ɗinka ƙunzugun don taimaka wa mata kasancewa cikin tsafta a lokacin jinin na wata-wata.
Asusun tallafa wa yara na Majalisar Ɗinkin Duniya ya fitar da wasu ƙa'idoji na yin ƙunzugun don tabbatar da sahihancinsa.
Haka kuma wasu maɗinka ƙunzugun sun shaida wa shirin Lafiya Zinariya abubuwan da mace ke buƙata domin yin ƙunzugun na tufafi.
Domin jin cikakken bayani latsa makunnin da ke sama don sauraron shirin.









