An dakatar da raflin Premier saboda kalaman cin mutuncin Liverpool da Klopp

Asalin hoton, Getty Images
An dakatar da alkalin Premier League, David Coote, bayan wani bidiyo da ya bayyana a kafar sada zumunta, inda yake kalaman cin mutunci ga Liverpool da Jurgen Klopp.
Mahukuntan Premier League sun ce sun dakatar da raflin ne, domin samun damar ci gaba da bincike kafin su fitar da matsaya kan batun.
Kawo yanzu BBC ba ta fayyace ingancin bidiyon ba da wajen da aka dauke shi, wanda yake ta zagaya kafar sada zumunta.
Coote, mai shekara 42 shi ne ya busa wasan Liverpool da ta doke Aston Villa 2-0 ranar Asabar a babbar gasar tamaula ta Premier League.
Raflin ɗaya ne daga fitattun masu alkalancin gasar Premier League da yake nuna ƙwarewa tun daga 2018.
To sai dai bidiyon da ke yawo a kafar sada zumunta ya danganci alkalancin Premier League da Coote ya yi a wasan da aka tashi 1-1 tsakanin Liverpool da Burnley a Yulin 2020.
Bayan tashi daga karawar Klopp ya caccaki Coote da cewar raflin baya busa laifi idan an yi wa ƴan ƙwallon Liverpool keta a fafatawar.
BBC ta tuntuɓi kwamitin da yake bitar ƙwazon alkalancin wasannin mako-mako a Premier League, domin karin bayani.











