Isra'ila ta kai hare-hare Iran da Iraqi da Syria

Ayatullah

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Gidan talabijin na gwamnatin Iran ya bayar da rahoton fashe-fashe da aka samu a birnin Isfahan, a kusa da babban filin jirgin saman kasar.

Haka kuma an ji fashewa a wasu wuraren a kasar ta Iran da Iraqi da kuma Syria.

Akwai alamun da ke nuna cewa hare-haren ramuwar gayya ne na Isra'ila, kan harin da Iran din ta kai mata kwana shida baya.

Daman duk tsawon mako ana ta hasashe a kan lokaci da kuma yadda Isra’ila za ta mayar da martani kan harin ba-zata da ba a taba gani ba wanda Iran ta kai mata- harin da ya fito yakin fakaice da dadaddun abokan gabar biyu ke yi a tsakaninsu fili.

A yanzu kafar yada labaran Iran ta ruwaito cewa an ji karar fashe-fashe a kusa da wani sansanin soji a birnin Isfahan, lamarin da ya sa aka dana garkuwar kariya ta sama ta birnin da ma sauran birane na kasar ta Iran.

Hotunan bidiyo da aka sanya a shafukan intanet sun nuna yadda ake ta harba makamai masu linzami na kare Iran ta sama.

Wani mai karnta labarai a tashar talabijin ta kasar, ya bayar da labarin fashewar:

Ya ce, kafofin labarai sun ruwaito cewa an ji karar fashewa mai girma a lardin Isfahan. Zuwa yanzu ba akai ga sanar da dalilin karar ba. Hukumomin yankin sun ce suna gudanar da bincike a kan lamarin.

Rahotanni sun ce an dakatar da zirga zirgar jiragen sama a biranen Iran da dama.

A ranar Asabar da daddare ne dai Iran ta harba wa Isra’ila makamai masu linzami da jirage marassa matuka na sama 300.

Da taimakon kawayen Isra'ilar an yi nasarar kakkabe da damansu kafin su kai ga Isra’ilar.

Jamian Israilar sun nuna cewa za su kai hari Iran din domin ramuwar gayya da kuma taka mata birki.

Shugabannin duniya suna ta kira ga Israilar da ta kai zuciya nesa a martanin nata don gudun kada lamarin ya fantsama a yankin na gabas ta tsakiya.

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadin cewa yankin na Gabas ta tsakiya na cikin wani yanayi mai matukar hadari.

Iran ta ce ba ta yi asarar komai ba sakamakon fashewar.

Ta yaya gaba tsakanin Isra'ila da Iran ta fara?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Dangantaka tsakanin Isra'ila da Iran na cikin yanayi mai kyau har sai a shekarar 1979, lokacin da dakarun juyin-juya halin Musulunci suka kwace mulki a Tehran.

Duk da cewa ta nuna adawa da batun raba Falasɗinu, wanda ya janyo kirkiro da ƙasar Isra'ila a 1948, Iran ta kasance ƙasar Musulmi ta biyu da ta amince da su, bayan Masar.

A wancan lokaci, ƴan gidan sarautar Pahlavi ne ke mulkar Iran, waɗanda suka kasance ɗaya daga cikin ƙawayen Amurka a Gabas ta Tsakiya. A kan wannan dalili, wanda ya kirkiro da Isra'ila da kuma shugaban gwamnatinta na farko, David Ben-Gurion, suka ƙulla abota da Iran a matsayin wata hanya ta magance batun kin amincewa da sabuwar ƙasar Yahudawa daga makwabtanta Larabawa.

Sai dai a 1979, juyin-juya halin Ayatollah Khomeini ya janyo hamɓarar da mulkin Shah da kuma assasa Jamhuriyar Musulunci wadda ta gabatar da kanta a matsayin mai kare hakkin waɗanda aka tsangwama.

Ɗaya daga cikin abin da ake gane sabuwar gwamnatin shi ne kin amincewa da katsalandan ko tursasawar Amurka da ƙawarta Isra'ila.

..

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Khomeini da sauran jagororin juyin-juya halin Musulunci sun kasance masu tausaya wa al'ummar Falasɗinu a kan Isra'ila

Sabuwar gwamnatin ta Ayattolah ta katse dangantaka da Isra'ila, ta kuma daina amincewa da sahihancin fasfo ɗin ƴan ƙasarta da kuma kwace iko da ofishin jakadancin Isra'ila a Tehran da miƙa shi ga Falasɗinawa, wadda a lokacin ke jagorantar gwagwarmayar kafa ƙasar Falasɗinu da adawa da gwamnatin Isra'ila.

Alí Vaez, jagoran wani shiri a Iran na ƙungiyar ICG, wadda ƙungiya ce mai zaman kanta da ke neman warware rikici a duniya, ya shaida wa BBC cewa nuna kiyayya kan Isra'ila na ɗaya daga cikin abubuwan da gwamnatin Iran a wancan lokaci ta zo da shi, saboda yawancin jagororinta sun taya Falasɗinwa yaƙin sari-ka-noke a wurare kamar Lebanon, kuma suna jin tausayinsu.

Sai dai, Vaez ya yi imanin cewa, "sabuwar Iran na son gabatar da kanta a matsayin kasar Musulunci mai karfi wadda kuma ta bijiro da batun kafa ƙasar Falasɗinawa da ƙasashen Musulmi suka watsar.

Ta wannan hanyar, Khamenei ya fara nuna cewa batun kirkiro da ƙasar Falasɗinawa tasa ce kuma an koma mara wa masu zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa a Tehran baya.

..

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Zanga-zangar adawa da Isra'ila ta zama ruwan-dare a Tehran

Vaez ya bayyana cewa ba a fara nuna kiyayya kan Iran a Isra'ila ba, sai a shekarun 1990, saboda a baya ana ganin shugaban Iraƙi Saddam Husseini a matsayin babbar barazana a yankin.

Gwamnatin Isra'ila na ɗaya daga cikin masu shiga tsakani da suka taimaka wa wani shiri mai suna 'Iran-Contra', wadda ta dalilinsa ne Amurka ta karkatar da makamai zuwa Isra'ila domin ta yi amfani da su a yaƙin da ta yi da makwabciyarta Iraƙi tsakanin 1980 da 1988.

Sai dai a tsawon lokaci, Isra'ila ta fara ganin Iran a matsayin ɗaya daga cikin masu barazana ga kasancewarta, inda gabar da ke tsakaninsu ta tashi daga cacar-baki zuwa gwabzawa.

Yaƙin 'sunƙuru' tsakanin Isra'ila da Iran

Vaez ya bayyana cewa, bayan da Iran ta fara ganin an zamar da ita saniyar ware musamman a irin ƙasashe kamar Saudiyya, wadda ke da karfi a yankin Gabas Ta Tsakiya, daga nan ta fara bijiro da tsare-tsare da zimmar dakatar da makiyanta daga kai mata hare-hare.

Isra'ila ba ta zauna haka kawai ba, inda ita da Iran suka yi ta kai wa juna hare-hare.

An kwatanta faɗa tsakanin Iran da Isra'ila a matsayin yaƙin sunkuru saboda duka ƙasashen sun kai wa juna hare-hare, inda a yawan lokuta ba tare da gwamnati ta bayyana hannunta a hukumance ba.

A 1992, ƙungiyar Jihadi Islamic Jihad, kusa da Iran, ta far wa ofishin jakadancin Isra'ila a Buenos Aires, abin da ya janyo mutuwar mutum 29. Jim kaɗan kafin haka, aka yi wa shugaban Hezbollah Abbas al-Musawi kisan gilla.

Wani abu da ke damun Isra'ila, shi ne ganin hanyar da za ta bi wajen dakile shirin nukiliyar Iran da kuma hana ƙasar samun muggan makamai.

..

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, isra'ila ta daɗe tana son daƙile shirin nukiliyar Iran

Tehran ta kuma ɗora laifin kai harin kan jami'an leƙen asirin Isra'ila.

Isra'ila tare da ƙawayenta na yamma, ta zargi Iran da kai mata hare-haren jirage marasa matuki da kuma na roka a baya, da kuma wasu hare-hare ta intanet.

Yaƙin basasar Siriya wadda ta faro a 2011, na ɗaya daga cikin abin ya janyo takun tsaka.

Majiyoyin leƙen asiri na ƙasashen yamma sun ce Iran ta tura makamai, kuɗi da kuma kwararru domin mara wa dakarun shugaba Bashar al Assad kan ƴan tawaye da ke ƙoƙarin hamɓarar da gwamnatinsa.

Hakan ya sanya hankula suka tashi a Isra'ila, wadda ta yi imanin cewa makwabtanta Siriya na cikin hanyoyin da Iran ke bi wajen aika makamai da kayan yaƙi ga Hezbollab a Lebanon.

Yaƙin 'sunkurun' ya kai bakin teku a 2021. A wancan shekarar, Isra'ila ta zargi Iran da kai wa jiragenta hare-hare a tekun Oman.

Iran, a nata ɓangaren, ta zargi Isra'ila da far wa jiragenta a tekun Bahar Mahaliya.

..

Asalin hoton, Getty Images

A shirye muke mu zauna a teburin sulhu - Raisi

..

Asalin hoton, Getty Images

Shugaban ƙasar Iran Ebrahim Raisi ya ce ƙasarsa ta shirya tattaunawar sulhu.

Mista Raisi ya ce "idan kai mai yawan surutu ne da ɓaɓatu, to mu ba haka muke ba, kuma ba mu bar teburin sulhu ba."

A lokaci guda kuma, ya ce "yaren da ake amfani da shi domin tunzura Iran ba zai karya mana gwiwa ba."

Ebrahim Raisi ya kwatanta manufofin harkokin wajen ƙasar da na lokacin Hassan Rouhani yana cewa lokacin da mutum zai nemi cinikayya kan makamanmu, kuma a yi shi yadda ya ga dama."

"Jiya, wasu mutane sun ce, ba za mu iya rubuta taken mutuwar Isra'ila ba da makamai, wanda zai janyo zaman ɗarɗar ga makiyanmu, amma yau makaman rokarmu za su iya sauka a tsakiyar birnin maƙiyanmu domin su fahinci laifukan da suke yi da kuma kisan kiyashin da suke yi."