United ta bai wa Onana hutu a wasan da Newcastle

Andre Onana

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United ta ajiye mai tsaron ragarta, Andre Onana a wasan da ƙungiyar za ta kara da Newcastle a gasar Premier League a yau Lahadi.

Onana ya tafka kura-kurai da suka janyo ƙungiyarsa buga kunnen doki, 2-2 a gasar Zakarun Turai ta Europa, kwana guda bayan tsohon ɗan wasan ƙungiyar, Nemanja Matic ya bayyana shi da ''ɗaya daga cikin masu tsaron raga marasa inganci''.

Wasu majiyoyi daga ƙungiyar sun ce an cire Onana daga tawagar ne domin ''ba shi damar hutawa don dawo da ƙarsashinsa''.

Ana sa ran ɗan wasan zai fuskanci ƙalubalen saka shi cikin tawagar da za ta kara da Lyon a wasan kwata fayinal na gasar Zakarun Turai ta Europa a ranar Alhamis.

Cikin wasa 43 da Onana ya buga a kakar bana, sau 10 ne kawai ƙwallo ba ta shiga ragarsa ba.