Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Labaran ƙarya da aka yaɗa a kan harin da aka kai wa mijin Nancy Pelosi
Wani mutum ya ji wa Paul Pelosi, mijin shugabar majalisar dokokin Amurka Nancy Pelosi rauni da guduma, a lokacin da ya kutsa gidan ma'auratan a San Francisco da safiyar Juma'ar da ta gabata.
Sa'o'i kaɗan bayan kai harin sai jerin labaran ƙarya suka fara yaɗuwa waɗanda ke cin karo da bayanan da ƴan sanda suka bayar kan abin da ya faru a lokacin harin.
Waɗannan jerin ikiraran na ƙarya tun tuni suka yadu kamar wutar daji bayan da sabon shugaban Tuwita Elon Musk da wasu masu faɗa a ji na jam'iyyar conservative suka ruruta zancen.
BBC ta yi duba tare da fayyace wasu daga cikin maganganun da aka yada kan harin.
Labarin ƙarya na batun luwaɗi
Ɗaya daga cikin saƙonnin ƙaryar da suka fi yaɗuwa kamar wutar daji kan harin shi ne wanda aka ce Mista Pelosi mai shekara 82 da maharin David DePape mai shekara 42, suna mu'amala ta luwadi sannan sun yi faɗa bayan da suka yi tatul da barasa.
Sai kuma aka yaɗa wasu bayanan da ba su zo daidai da waɗanda hukuma ta fitar ba don kafa hujja kan batun farkon.
Waɗannan labaran sun fara tashe ne a Amurka bayan da Elon Musk ya wallafa wani labari daga shafinsa na intanet yana yaɗa irin wannan zargi ga mabiyansa miliyan 112 a ranar Lahadi, kafin daga baya ya goge saƙon ba tare da ƙrin bayani ba.
"Akwai yiwuwar bayanan da aka gano dangane da batun nan ɗan kaɗan ne, akwai abin da ya fi hakan," kamar yadda Mista Musk ya faɗa a martanin da ya mayar wa saƙon Hillary Clinton.
Shafin intanet ɗin da Mista Musk ya yaɗa labarin daga can ya yi ƙaurin suna wajen wallafa labaran ƙarya ciki har da wani labari da aka wallafa a shekarar 2016 da ke cewa Hillary Clinton ta mutu.
Ɗaya daga cikin ƙarerayin na intanet shi ne wanda ke cewa Mista Pelosi da maharin Mr DePape suna sanye ne kawai da gajerun wanda a lokacin da ƴan sanda suka isa gidan.
Amma saƙon ƙorafin da aka tra wa FBI na cewa Mr DePape yana sanye ne cikin baƙaƙen kaya siɗik daga sama har ƙasa.
Wani labarin kuwa cewa yake dama can mutanen biyu sun san juna kafin harin kuma abokai ne.
Wata ƴar majalisar dokoki ta jam'iyyar Republican Marjorie Taylor Greene ta nanata labarin a wani saƙon tuwita a jiya.
FBI ta ce a ƙorafin da aka gabatar mata, Paul Pelosi bai taɓa sanin Mr DePape ba.
Mr Pelosi ya yi amfani da dabara ne wajen aika sƙo ga lambar gaggawa ta 911 daga banɗaki, kuma nan da nan mai amsa wayar ya gano abin da ke faruwa a gidan a lokacin.
Wata jita-jitar da ke ƙara son tabbatar da labarin cewa sun san junan, shi ne ganin gilashin gidan da aka tarwatsa ɗin daga ciki ne ba daga waje ba, abin da ke nuna cewa Mr Pelosi yana sane ya bar Mr DePape ya shiga.
Tsohon shugaban ƙasar Donald Trump ya faɗi hakan a wata hira ta baya-bayan nan, inda yake cewa "ba fasa gidan aka yi aka shiga ba, daga ciki aka fasa."
Sai dai ƙorafin da aka tura wa FBI cewa aka yi wani ya fasa gilashi ya shiga gidan, wanda hakan abu ne mai wahala sai an haɗa da guduma."
Babu wata shaida daga bayanan ƴan sanda cewa akwai wnai mutum na uku a gidan a lokacin harin.
Batun shafukan intanet na maharin ƙarya ne
An gano wasu shafukan intanet masu sunan maharin bayan da ƴan sanda suka bayyana sunansa bayan faruwar harin, wadanda suka an cire su daga baya.
Rubuce-rubucensa waɗanda BBC ta gani, sun nuna cewa shi ɗin mutum ne da yake nda aƙidar tsattsauran ra'ayi.
Yakan yi rubuce-rubucensa ne a kan fannoni da dama da suka haɗa da bayanai kan cewa an yi maguɗi a zaɓen 2020, da batun rikicin da aka yi a majalisar dokoki na Capitol a ran 6 ga watan Janairu, da ikirarin cewa riga-kagfin korona na da illa da kuma batu kan nuna wariyar launi da ƙin jinin Yahudawa.
Wasu bayanai na intanet sun nuna cewa labaran shafukan nasa ƙarya ne kuma a ranar da harin ya faru ne aka ƙirƙire su.
Amma BBC tana da hoton abubuwan da ya wallafa a shafin nasa da ke nuna cewa tun a watan Agusta ya wallafa su, makonni kafin kai harin.
Wasu kuma sun ma ce Mr DePape ya kai harin ne saoda aƙidunsa ta siyasa.
Wani mai sharhi kuma mai ra'ayin riƙau Matt Walsh ya ce "ba daidai ba ne" a bayyana maharin a matsayin "sojin sa kai mai ra'ayin riƙau."
Sanatan Texas Ted Cruz ya jadda kalaman na Mr Walsh a wani saƙon tuwita da cewa "gaskiyar magana" kenan.
Sai dai ƙorafin ƴan sanda ya nuna cewa da gayya aka kai harin.
Atoni na gundumar San Francisco, Brooke Jenkins, ya ce harin ya fi kama da "mai alaƙa da siyasa."
A hirarsa da ƴan sanda, Mr DePape ya bayyana Nancy Pelosi a matsayin "mashahuriyar maƙaryaci," inda ya ƙara da cewa da ya same ta da ya karya mata gwiwa.
Ko a baya-bayan nan abokan hamayyar siyasa sun yi ƙoƙarin kai wa wani ɗan majalisa Steve Scalise da Alkalin Kotun Ƙoli Brett Kavanaugh hari.
Da'awoyi marasa tushe
Da'awoyi marasa tushe a duk lokacin da aka kai hari, ba su taƙaita ga masu tsattsauranra'ayi ba.
Wasu masu sassauƙan ra'ayin sun yi yaɗa wani saƙon tuwita da wata ƴar majalisa Marjorie Taylor Greene, ta wallafa kwana ɗaya kafin harin da ke cewa: "Ku jira har sai gobe."
Wasu mutanen da dama sun yi ta nuna cewa saƙon tuwitar na Ms Taylor Greene ka iya zama alama ta cewa tana sane da harin da aka kai gidan Pelosi.
Sai dai babu wata hujja da za ta tabbatar da wannan ikirari.