Arsenal ta fara da cin ƙwallo biyu a makon farko a Premier

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal ta fara kakar bana da cin Wolverhampton 2-0 a wasan makon farko a Premier League ranar Asabar a Emirates.
Kai Havert ne ya fara ci wa Gunners ƙwallon, bayan da Bukayo Saka ya bugo masa tamaula daga baya Saka ɗan wasan tawagar Ingila ya kara na biyu.
Arsenal, wadda ke fatan taka rawar gani a kakar bana ta rike ƙwallon yadda ya kamata, duk da kalubalen da ta fuskanta daga Wolves.
Sabon ɗan wasan da Wolves ta ɗauka, Jorgen Strand Larsen ya kusan cin ƙwallo, amma mai tsaron ragar Arsenal, David Raya yana wajen.
Lokacin da Wolves ke ta kokarin farke ƙwallon farko, Matheus Cunha ya samu dama mai ƙyau, sai dai Raya ya hana ƙwallon shiga raga.
Ƙungiyar da Gary O'Neil ke jan ragama ta yi iya kokarin ta zare kwallayen, amma Gunners ta riga ta shirya hada maki uku da ƙwallo biyu a raga a karawar.
Ranar Asabar 24 ga watan Agusta, Arsenal za ta je Aston Villa a wasan mako na biyu, yayin da Wolves za ta karɓi bakuncin Chelsea ranar Lahadi 27 ga watan nan.






