Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Varane ya sharbi kuka bayan rauni da ya ji a wasa da Chelsea
Dan wasan tawagar Faransa, Raphael Varane ya sharbi kuka, sakamakon raunin da ya ji a wasan Premier League da Chelsea ranar Asabar.
Chelsea ta karbi bakuncin United a karawar mako na 13 a babbar gasar tamaula ta Ingila, inda suka tashi 1-1 a Stamford Bridge.
Mai tsaron bayan ya ji rauni, bayan saura kasa da wata daya a fara gasar cin kofin duniya da Qatar za ta karbi bakunci.
Varane ya ji raunin ne a kokarin tare Pierre-Emerick Aubameyang na Chelsea, an kuma maye gurbinsa da Victor Lindelof.
Kociyan United, Erik ten Hag ya ce ya yi wuri a fayyace girman raunin da ya ji, saboda haka sai likitoci sun auna shi daga nan su bayyana komai.
Varane, wanda ya koma Old Trafford da taka leda daga Real Madrid a 2021 na fama da yawan jin rauni a wasannin da yake yi wa United.
Chelsea ce ta fara cin United a bugun daga kai sai mai tsaron raga ta hannun Jorginho saura minti uku lokaci ya cika.
United ta farke daf a tashi ta hannun sabon dan wasan da ta sayo a bana daga Real Madrid, Casemiro.
Chelsea tana mataki na hudu a teburin Premier League a kakar nan da tazarar maki daya tsakaninta da United ta biyar.
Za a fara gasar cin kofin duniya ranar 20 ga watan Nuwamba zuwa 18 ga watan Disamba.
Faransa ce mai rike da kofin, wadda ta dauka a Rasha a 2018.