Rashford ya bukaci masu gulmar makomarsa a United su bari

Marcus Rashford

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Marcus Rashford ya yi kira ga masu gulmarsa kan makomarsa a Manchester United da su daina, bayan da bai buga karawa da Fulham ba, sakamakon jinya.

Koci, Erik ten Hag ya caccaki Rashford, wanda ya je ya yi bikin cikar ranar haihuwarsa awanni tsakani, bayan da Manchester City ta doke su 3-0 a Premier.

Sai dai Ten Hag ya sanar da manema labarai cewar dalilin da Rashford bai buga wasan Fulham ba, saboda yana jinya ne.

Dan wasan tawagar Ingila ya yi zaman benci a Carabao Cup da Newcastle United ta fitar da United, kwana uku tsakani da ta yi rashin nasara a hannun City.

Rashford shi ne kan gaba a ciwa United kwallye a kakar da ta wuce a bara, mai 30 a raga a dukkan fafatawa.

Sai dai kuma guda daya ya zura a raga tun fara kakar tamaula ta bana.

United ta yi rashin nasara a wasa biyar daga 11 da ta kara da fara Premier League a bana.

Sai dai kungiyar ta ci Fulham 1-0, hakan ya sa ta fara komawa hayyacinta, bayan da City da ta doke ta a Premier da fitar da ita da aka yi a Carabao Cup.