Inter Miami ta yi tuntuɓe a gasar MLS ta bana

An wallafa

Lionel Messi ne ya ci wa Inter Miami ƙwallon da suka tashi 1-1 da LA Galaxy ranar Lahadi.

Galaxy ta fara cin ƙwallo ne bayan mintuna 75 ta hannun ɗan wasanta Dejan Joveljic, kafin daga bisani aka bai wa ɗan wasan tsakiya Mark Delgado jan kati bayan ya karɓi katin gargaɗi guda biyu.

Sai da wasa ya kusa tashi ne Messi ya farke wa Miami tare da taimakon tsohon abokin wasansa na Barcelona Jordi Alba.

Miami ta doke Real Salt Lake a wasanta na farko a kakar wasan gasar Major League Soccar ta bana ta Amurka a makon jiya.

Inter Miami ce kan gaba a rukunin gasar ta yankin gabas da maki huɗu amma ita ce kaɗai ta buga wasanni biyu a rukunin . Ƙungiyar da ke hamayya da Miami, DC United ita ma ta fara kakar wasan bana da ƙafar dama inda ta doke New England Revolution da ci 3-1 a ranar Asabar.

A wani ɓangaren kuma, ƙungiyar da Phil Neville ke horaswa, Portland Timbers ta sami ɓagas inda ta doke Colorado Rapids da ci 4-1 a wasanta na farko na sabuwar kakar.

Nasarar a ranar Asabar ita ce ta farko da Neville ya samu tun bayan komawar sa MLS bayan Inter Miami ta kori tsohon ɗan wasan na Man U a watan Yuni.