Newcastle ta gwangwaje Guimares, Liveropool na tattaunawa da Mac Allister

An wallafa

Newcastle ta gabatar da tayin albashin £200,000 duk sati ga Bruno Guimaraes domin dauke hankalinsa kan Liverpool da Real Madrid da Barcelona da ke kwadayinsa. A yanzu ɗan kasar Brazil din mai shekara 25 zai kasance ɗan wasa mafi tsada a kungiyar.(Sun)

Liverpool na tattaunawa da ɗan wasan Argentina mai buga tsakiya, Alexis Mac Allister, ɗan shekara 24, domin dauke shi daga Brighton a mako mai zuwa. (Fabrizio Romano)

Joao Felix ya samu tayi da Newcastle a matsayin aro daga kungiyarsa ta Atletico Madrid kwanaki bayan Chelsea ta sauya ra'ayi kan cinikin ɗan wasan asalin Portugal mai shekara 23. (Mail)

Ruben Loftus-Cheek, mai shekara 27, ya amince ya bar Chelsea zuwa AC Milan. (La Gazzetta dello Sport via Sun)

Kyeftin din Ingila Harry Kane, mai shekara 29, na son tafiya Manchester United a wannan kaka, maimakon ya tafi wata kungiya a ketare, sai dai kuma yana iya hakuri har karshen kwantiraginsa kafin ya bar Tottenham a badi. (Sun)

Real Madrid na iya mika tayi kan Kane idan Karim Benzema mai shekara 35 ya amince da tayin da aka yi masa mai kwaɓi daga Saudiyya. (Times - subscription required)

Tottenham za ta sake zage damtse a farautar Ange Postecoglou bayan kungiyarsa ta Celtic ta kai wasan karshe na Scottish cup a ranar Asabar.(Evening Standard)

Chelsea za ta sayar da ɗan wasanta asalin Senegal Kalidou Koulibaly, mai shekara 31, wanda ta sayo daga Napoli kan £33m a bara. (Evening Standard)

Chelsea ta kuma bai wa Manchester City damar tattaunawa da ɗan wasanta asalin Croatia Mateo Kovacic, mai shekara 29. (Mail)

Manchester United da Barcelona da Inter Milan sun kwaɗaitu da ɗan wasan Faransa Benjamin Pavard, mai shekara 27, wanda ba shi da niyyar sabunta kwantiraginsa a Bayern Munich da ke karewa a 2024. (L'Equipe - in French)

Shugaban hukumar kwallonm kafa ta Saudiyya, Yasser Al-Misehal, ya ce zai so ganin kungiyarsu ta Al-Hilal ta hada wasa tsakanin Lionel Messi mai shekara 35 da kuma Cristiano Ronaldo mai shekara 38 da ya koma Al Nassr a watan Janairu. (SSC via Goal)

Wa'adin Sam Allardyce a matsayin kocin Leeds zai kare a ranar Alhamis, lokacin da tsohon kocin na Bolton da West Ham zai gana da manyan kungiyar. (Telegraph - subscription required)

Arsenal ta ninka albashin William Saliba kan kuɗin da ake ba shi kowanne mako a sabon kwantiraginsa, inda zai ke karban £120,000 a duk sati, saboda fargabar kar ya tafi Paris St-Germain. (Sun)