Liverpool ta ce Diaz ba na sayarwa ba ne, Walker na son zuwa Saudiyya

An wallafa

Arsenal na son danwasan gaba na Sweden mai taka leda a Sporting Lisbon Viktor Gyokeres, mai shekara 25, a kakar wasan bana. Kwantiragin tsohon danwasan Coventry ya kai fam miliyan 85. (Football Transfers)

Liverpool ta shaida wa Barcelona dan wasan Colombia Luis Diaz, mai shekara 27, na cikin tsarin kulub din, don haka ba na sayarwa ba ne. (Mirror)

Arsenal da Liverpool na son danwasan Eintracht Frankfurt kuma na tsakiyar Ecuador Willian Pacho, mai shekara 22. (90min)

Danwasan Arsenal na tsakiyar Ingila mai shekara 24, Reiss Nelson na sahun gaba cikin wadanda Brighton ke son dauka a kakar nan. (Teamtalk)

Manchester United na bukatar fam miliyan 43 kan danwasan gaba na Ingila Mason Greenwood, mai shekara 22, wanda ke zaman aro a kakar nan a kungiyar Getafe ta Sifaniya. Bayanai na cewa wani kulub daga Saudiyya na son danwasan na. (Mirror)

Manchester United na son dawo da tsohon danwasan tsakiya na Newcastle United Mikel Merino, 27 na Ingila. (COPE - in Spanish)

Duk da sha'awar da Juventus da AC Milan, suka nuna na son mai tsaron raga na Atletico Madrid Mario Hermoso mai shekara 28, ita ma Aston Villa na hakilon danwasan a kakar wasan bana. (calciomercato.com)

Watakila Chelsea za ta yi zubin sabbin 'yanwasa, amma kila danwasan gaba na Ingila Raheem Sterling, mai shekara 29 ya ci gaba da taka leda. (Mail)

West Ham na bibiyar danwasan Sporting Lisbon da Portugal Pedro Goncalves, mai shekara 25. Sai dai kwantiraginsa da Sporting zai kare ne a watan Yunin shekarar 2027. (Record - in Portuguese)