An fitar da Al-Nassr daga Champions League na Asia

An wallafa

Kungiyar Cristiano Ronaldo Al-Nassr ta yi waje a Champions League na Asia a zagayen daf da na kusa da na karshe, bayan rashin nasara a bugun fenariti a hannun Al-Ain.

Al-Nassr, wadda aka ci 1-0 a wasan farko ta yi nasarar cin 4-3 a gida da ta kai su bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Ronaldo ne kadai ya ci kwallon da Al-Ain ta yi nasara da cin 3-1 a bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Mai kyautar Ballon d'Or biyar, mai shekara 39 bai ji dadi da ya barar da wata dama da ya samu daga yadi na biyar.

Tsohon dan wasan Manchester United, Alex Telles shi ne ya ci wa Al-Ain kwallo na uku a minti na 72 da ta kai har zuwa bugun fenariti, bayan karin lokaci.

Al-Nassr ta kammala karawar da 'yan kwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Ayman Yahya jan kati.

Al-Ain, kungiya ce daga Hadaddiyar Daulal Larabawa ta kai zagayen gaba daga gasar ta zakarun Asia ta bana.