Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Chelsea za ta mamaye gasar Premier League nan gaba - Maresca
Koci, Enzo Maresca ya ce Chelsea za ta mamaye gasar Premier League nan da shekara biyar zuwa 10 masu zuwa.
Mai shekara 44, ya ce baya ganin Chelsea cikin masu damar lashe kofin bana, duk da ƙungiyar tana ta ukun teburi da maki iri ɗaya da na Arsenal ta biyu, bayan mako na 13.
Chelsea ta haura Manchester City mai Premier na bara a kan teburi a ranar Lahadi, bayan da ta doke Aston Villa 3-0, amma Liverpool, wadda take ta ɗaya ta ba ta tazarar maki tara tsakani.
Maresca baya sa Chelsea cikin waɗanda za su iya ɗaukar babban kofin gasar tamaula na Ingila na kakar nan, duk da maƙudan kuɗin da Todd Boehly ya fitar da aka sayo fitattun ƴan ƙwallo.
Chelsea ta kashe sama da £1.5bn wajen sayen sabbin ƴan wasa tun bayan da aka sayi ƙungiyar daga Roman Abrohimovich.
Kawo yanzu irinsu Enzo Fernandez da Moises Caicedo da Nicolas Jackson na kan ganiya da kuma Cole Palmer tun bayan wata 18.
Maresca ya ce ƙarancin shekarun ƴan wasan da yadda suke bukatar samun gogewa shi ya sa yake ganin ba za su iya taka rawar gani ba a kakar nan.
Chelsea ta kammala a mataki na 12 da na shida a kaka biyu baya, karkashin ƴan Amurka da suka mallaki ƙungiyar, wadda har yanzu ba ta ɗauki kofi ba.