Zaɓen Amurka: Wa ke sahun gaba tsakanin Harris da Trump?

Hoton Kamala Harris da Donald Trump. Kamala Harris a hannun dama sanye da kwat da farar bulawus, ta na daga hannu. Donald Trump ne a hannun hagu, sanye da kwat da fara r'yar ciki da nakitayal, ya dunkule hannunsa kamar dai yadda aka saba ganin ya na yi.
    • Marubuci, By The Visual Journalism & Data teams
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

A ranar 5 ga watan Nuwamba ne Amurkawa za su fita rumfunan zaɓe domin zaɓar shugaban ƙasa.

Ana kwatanta zaɓen da wanda aka gani a shekarar 2020, amma lamura sun sauya tun watan Yuli lokacin da shugaba Biden ya sanar da janye daga neman wa'adin mulki na biyu tare da mara baya ga mataimakiyarsa Kamala Harris.

Babbar tambayar da kowa ke yi ita ce shin Amurkawa za su yi shugabar ƙasa mace, ko kuwa za su zaɓi Donald Trump?

Yayin da lokacin zaɓe ke karatowa, za mu ci gaba da kawo muku bayanai dalla-dallah kan yadda gangamin yaƙin neman zaɓen ke gudana a kokawar shiga fadar White House.

Kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta ƙasa?

Harris na sahun gaba da 'yar tazara kaɗan tsakaninta da Trump, a kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta ƙasa tun karshen watan Yuli, kuma har yanzu dai a sahun gaba take kamar yadda za ku gani a bayanan da suke ƙasa wadda kididdiga ce ta baya-bayan nan da aka yi.

Harris ta samu tagomashi a kuri'ar jin ra'ayin jama'a a makonnin farko na fara gangamin yaƙin zaɓenta, tana bunƙasa sannu a hankali tana ƙara sama har zuwa karshen watan Agusta da ta bai wa abokin hamayyarta ratar kashi 4 cikin 100.

To amma tun watan Satumba da ya wuce komai ke tafiya babu tangarɗa, hatta bayan muhawarar 'yan takarar shugaban ƙasa da suka yi da Trump, wadda kusan mutane miliyan 70 suka kalla.

Idan aka yi lura cikin tsanaki za a ga ƙaruwar bata taka kara ta karya ba tun daga wannan lokacin a kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta kasa a makonnin da ya gabata, inda alamu suka nuna mafi kankanta da kankan da 'yan takarar biyu suka bai wa juna.

Ya kamata a lura wannan kididdigar ta kuri'ar kasa tana da muhimmanci, kuma wata hanya ce ta sanin farin jinin 'yan takarar a ɗaukacin Amurka, sai dai ba lallai su zama cikakkiyar hanyar da za a yi hasashen sakamakon zaɓen shugaban kasa da ke tafe ba.

Dalilin shi ne, Amurka na amfani da kuri'u na musamman da aka bai wa kowacce jiha kuri'u ta amfani da girma da yawan jama'arsa.

Baki-ɗaya kuri'un na musamman guda 538 su ne tsanin da ɗan takara ke buƙata, dan haka aƙalla ɗan takara na buƙatar kuri'u 270 da zai kai shi ga nasara.

Amurka na da jihohi 50, amma saboda kusan dukkan jihohin na zaɓar jam'iyya guda ne, a zahiri kowanne ɗan takara na da damar samun nasara a kuri'un.

Waɗannan su ne wuraren da za a iya cin zaɓen ko faɗuwa, ana yi wa kuri'un nan lakabi da tsantsar rabo, ana kuma yi wa jihohin lakabi da a lallaɓa.

Wane ne zai yi nasara a jihohi a lallaɓa?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A yanzu dai ana tafiyar ne kafaɗa da kafaɗa tsakanin 'yan takarar biyu a jihohin bakwai da ake faɗan karshen, ko dai ɗan takara ya yi nasara da gagarumin rinjaye, ko ya sha da kyar kamar yadda masu hasashen kuri'un suka camfa.

Idan akai duban tsanaki daga lokacin da Harris ta shiga yaƙin neman zaɓen, babu wani abin a zo a gani da ya faru a jihohin nan bakwai na wanke hannu ka taɓa ko a lallaɓa, amma yana da muhimmanci mu san za a iya samun bambance-bambance tsakanin jihohin ta fuskar yawan kuri'un da za a samu, wasu masu yawa wasu kuma akasin hakan.

A jihar Arizona, da Georgia da North Carolina, an samu sauyi kan wanda ke sahun gaba, da farko a watan Agusta tsohon shugaban ƙasa Donald Trump ne ke sahun gaba, yanzu kuma ya samu koma baya kaɗan.

Harwa yau, an ga haka a jihar Nevada inda Harris ta ɗan yi gaba da 'yar tazara.

A sauran jihohin uku wato Michigan, da Pennsylvania da Wisconsin - tun a watan Agusta Harris ce ke sahun gaba da maki aƙalla biyu zuwa uku, amma a kwanakin da suka gabata lamarin ya sauya.

Dukkan jihohin uku makarfafar jam'iyyar Democrat ce kafin Trump ya ba su kashi a shekarar 2016, da ya shayar da su mamakin zama shugaban Amurka.

A shekarar 2020 kwatsam sai Joe Biden ya sake karɓe jihohin, idan har Harris za ta iya abin da ya yi to lallai za ta iya kai labari a lashe zaɓen.

Tun daga lokacin da Harris ta shigo yakin neman zaɓen aka fara ganin sauye-sauye, jim kaɗan bayan tsayar da ita 'yar takara karkashin jam'iyya mai mulki.

A wannan ranar da Biden ya janye daga takarar, Trump na gaba da shi da maki kusan biyar a dukkan jihohin bakwai.

A jihar Pennsylvania, Biden na baya da sama da kashi huɗu a lokacin da ya janye daga takarar shugaban ƙasa, kamar yadda taswirar da ke ƙasa ta nuna.

Wannan jiha ce mai matukar muhimmanci tun daga lokacin yakin neman zaɓe, har zuwa ranar zaɓen da kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta 'yan kasa, sai da wannan nasarar sannan za a samu wanda ya yi nasarar zama shugaban Amurka.

Ta yaya ake samar da waɗannan mafi kankantar?

Kididdigar da muka yi amfani da ita da hotunan sama a shafin intanet, na sharhi kan kididdigar kuri'ar jin ra'ayi ta ƙasa, wadda ta na daga cikin kafar yaɗa labaran Amurka ABC.

Domin samar da ita an karɓo bayanai har 538 daga kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta ƙasa daban-daban, musamman jihohin da ake ganin su ne masu zafi da wuyar sha'ani.

A wani mataki na nuna iko, ana buƙatar kuri'u 530 ciki har da na kamfanonin da suka cika wasu ka'idoji su ma za su samu damar ba da ta su kuri'ar, dole a tabbatar da sahihancin kuri'un, ko dai ta wayar tarho, ko sakon intanet ko kuma sakon wayar salula.

Shin za mu iya amincewa da wannan kuri'a?

A halin yanzu, sakamakon na nuna cewa Kamala Harris da Donald Trump suna tafiya kafaɗa da kafaɗa, ko da an samu tazara tsakaninsu, ba a jimawa suke sake yin kunnen doki, idan ana tafiya irin hakan da wuya a gane ko yin hasashen wanda zai yi nasara.

Abin nan da ake cewa ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare.

Ana auna farin jinin Donald Trump daga shekarar 2016 da 2020. Kamfanonin da ke kula da zaɓen za su yi kokarin magance matsalolin da aka samu a wancan lokacin da suka haɗa da tafiyar hawainiya lokacin kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta ƙasa.

Waɗannan dai sauye-sauye ne da za su yi tasiri a tabbatar da an gudanar da zaɓen cikin nasara.

Ranar 5 ga watan Nuwamba Amurkawa za su fita rumfunan zaɓe domin tantance tsakanin tsaki da tsakuwa, ko dai a sake zaɓar Donald Trump, ko kuma zaɓar mace ta farko a matsayin shugabar kasa.