Modric ya yi kan-kan-kan da Benzema a yawan buga gasar zakarun Turai

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ƙyaftin ɗin Real Madrid, Luca Modric ya buga wasa na 133 a Champions League ranar Talata a Emirates.

Kenan ya yi kan-kan-kan da Karim Benzema a mataki na biyu a Real Madrid a jerin waɗan da suka buga mata gasar zakarun Turai da yawa a tarihi.

Real ta yi rashin nasara 3-0 a gidan Arsenal da ci 3-0 a wasan farko zagayen kwata fainal da suka barje gumi.

Tun farko Benzema shi ne na biyu a yawan yi wa Real wasa da yawa a Champions League, yana saman Raul Gonzalez mai 132, Iker Casillas ne na farko mai karawa 152.

Cikin wasa 133 da Modric ya yi a Real a gasar zakarun Turai, an yi nasara 84 da shi a cikin fili da canjaras 23 da rashin nasara 26.

Modric gwarzo ne a Real Madrid, wanda ɗaya ne daga ƴan wasa biyar da suka lashe Champions League shida a tarihi, wanda ya ɗauka a 2014 da 2016 da 2017 da 2018 da 2022 da kuma 2024.

Ƴan Real 10 da suka kan gaba a yawan buga gasar zakarun Turai:

  • Casillas 152
  • Modrić 133
  • Benzema 133
  • Raúl 132
  • Sergio Ramos 129
  • Kroos 110
  • Roberto Carlos 109
  • Marcelo 102
  • Cristiano Ronaldo 101
  • Guti 99