Jam'iyyu 14 da INEC ta zaɓa domin yi wa rijista

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar zaɓe ta Najeriya ta ce ta zaɓi wasu ƙungiyoyi guda 14 da take ganin za ta yi wa rijistar zama jam'iyyun siyasa bayan dacewa da dukkannin sharuɗɗan da ta gindaya.
Jami'ar hukumar, Zainab Aminu, ta shaida wa BBC cewa ta tantance ƙungiyoyin ne daga fiye da 170 da ke neman rijistan zama jam'iyyun siyasa a Najeriya, inda ta ce an yi watsi da guda 157.
Sai dai hukumar ta ce hakan ba wai yana nufin kai tsaye za mu samu rijistar zama jam'iyyun siyasa ba ne kai tsaye.
"Za mu gayyace su mu sake tantance su domin tabbatar da cika dukkan sharaɗɗa da suka haɗa da ofishin ƙungiya da manufofi da sauransu." In ji Zainab Aminu.
Jerin sunayen jam'iyyu 14
Jam'iyyun 14 da INEC ta ce ta zaɓa domin yi wa rijista su ne:
- African Transformation Party
- All Democratic Alliance
- Advance Nigeria Congress
- Abundance Social Party
- The African Alliance Party
- Citizens Democratic Alliance
- Democratic Leadership Alliance
- Grassroots Initiative Party
- Green Future Party
- Liberation People's Party
- National Democratic Party
- National Reform Party
- Patriotic Peoples Alliance
- Peoples Freedom Party
Nawa ne jam'iyyun siyasa a Najeriya?
Najeriya dai na bin tafarkin jam'iyyu da yawa duk da cewa a kan samu guda biyu zuwa uku da suke fi rinjaye sannan aka fi magana a kansu.
A yanzu haka dai akwai jam'iyyu 18 da hukumar zaɓe ta Najeriya ta san da zamansu, bayan cire wasu fiye da 70 daga rijistar kasancewarsu jam'iyyu sakamakon rashin yin kataɓus a zaɓen 2023.
- Accord (A)
- Action Alliance (AA)
- African Action Congress (AAC)
- African Democratic Congress (ADC)
- Action Democratic Party (ADP)
- All Progressive Grand Alliance (APGA)
- Allied Peoples Movement (APM)
- Action Peoples Party (APP)
- Boot Party (BP)
- Labour Party (LP)
- National Rescue Movement (NRM)
- New Nigeria Peoples Party (NNPP)
- Peoples Democratic Party (PDP)
- Peoples Redemption Party (PRP)
- Social Democratic Party (SDP)
- Young Progressive Party (YPP)
- Youth Party (YP)
- Zenith Labour (ZLP)
Hakan na nufin idan har hukumar zaɓen ta sahhalewa dukkannin ƙungiyoyi 14 da take tantancewa a matsayin jam'iyyu to Najeriya za ta zama mai yawan jam'iyyu 32.
Jam'iyyu nawa ne suka kamaci Najeriya?
Farfesa Abubakar Kari Malami a jami'ar Abuja kuma masanin kimiyyar siyasa ya ce tsarin da ya fi dacewa da siyasar Najeriya shi ne samun jam'iyyu da dama, amma kada su wuce kima.
''A ƙasa irin Najeriya yana da kyau a yi jam'iyyu da dama, amma kuma yana da kyau a samar da dokoki masu tsauri ta yadda ba za su yi yawa ba su zama Inna ruddudu''. in ji shi.
Sai dai kuma Malam Kabiru Sa'idu Sufi malami a kwalejin share fagen shiga jami'a a Kano, CAS ya ce tsarin jam'iyyun da dama shi ya fi dacewa da Najeriya, domin gudun danne wa wasu ƴanƙasar dama.
''Rashin bayar da damar kan sa wasu su riƙa yi wa dimokraɗiyyar zagon ƙasa... amma dai yana da kyau a kula kada jam'iyyun su yi yawan da za su zama matsala'', in ji shi.










