Su wane ne za su iya maye gubin Ten Hag a Man United

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United ta kori kocinta Erik Ten Hag bayan da ƙungiyar ta ci gaba da samun matsala a kakar wasa ta bana.
Ta sha kashi da ci 2-1 a hannun West Ham United ranar Lahadi, sakamakon da ya sa ta tsinci kanta a matsayi na 14 a teburin Premier ta bana.
Rashin nasarar ya zo ne kwana uku bayan United ta yi canjaras da Fenerbahce a gasar kofin Europa League.
Ten Hag ya rattaba hannu kan sabon kwantiragi a bazara, kuma ya bar Old Trafford bayan shekaru biyu da rabi yana jan ragamar ƙungiyar.
A halin yanzu dai an fara hasashen ko waye zai iya maye gurbinnsa a kulob ɗin.
Ruud van Nistelrooy
Tsohon ɗan wasan na Manchester United ya koma ƙungiyar a bazarar da ta gabata, ya zama mataimakin Ten Hag bayan wani garambawul da aka yi wa ɓangaren horaswa na kulob ɗin - kuma yanzu shi zai karɓi ragamar ƙungiyar na wucin gadi.
Nistelrooy ya yi zaman kakar wasa biyar a matsayin ɗan wasan gaba a ƙungiyar bayan da ya koma United a shekarar 2001, inda ya zura ƙwallaye 150 – adadin da ya sa ya zama na 11 a jerin suka fi zura ƙwallaye a tarihin kulob ɗin.
Kafin komawarsa United a bazara bai yi wani aiki ba tun lokacin da ya bar aikinsa na kocin PSV Eindhoven kafin ƙarshen kakar wasa ta 2022-23, bayan ya lashe Kofin Holland a wa'adinsa na farko.
Kocin mai shekara 48 ya kuma yi aiki sau biyu a matsayin mataimakin koci a tawagar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Netherlands.
Amma ko rashin gogewarsa a matsayin koci da kuma kasancewarsa a tawagar Ten Hag zai iya kawo masa cikas a yunƙurinsa na zama kocin United na dindindin?
Graham Potter
Lokacin da Chelsea ta sallame shi a watan Afrilun 2023, mutane da dama ba su yi tunanin Potter zai daɗe bai samu wani aiki ba. Amma haka lamarin ya kasance bayan kusan watanni 18.
Ɗan takaitaccen zaman da Potter ya yi a Stamford Bridge bai yi tasiri ba a yayin da aka yi wa ƙungiyar gyaran fuska, amma a baya ya samu yabo sosai kan aikin da ya yi a Brighton, tun da farko dai ya taɓa kasancewa kocin kulob ɗin Ostersund na Sweden da Swansea.
Kocin mai shekara 49 ya ɗaukaka Brighton zuwa matakin Firimiya a cikin shekaru uku kuma sunansa kan ɓullo a duk lokacin da aka samu gurbi a duk wani babban aikin horaswa - ciki har da mukamin kocin Ingila.
Kafin rashin tasirin da ya yi a Chelsea, mutane da yawa sun bayyana Potter a matsayin koci mafi kwarewa a saboda yadda ya ɗaukaka Brighton.
Ya kuma yi aiki tare da darektan ƙwallon ƙafa na United Ashworth a filin wasa na Amex, kuma kwanan nan ya ce a shirye yake ya koma aikin horaswa.
Thomas Frank
Ana mutunta kocin ɗan ƙasar Denmark saboda aikin da ya yi na hauro da Brentford zuwa gasar Premier sannan kuma ya ƙarfafa matsayinta a gasar.
har yanzu Frank mai shekaru 50 yana tare da ƙungiyar duk da ana ambatonsa a duk lokacin da babban aiki ya samu, amma ana ganin sai United ta yi wani gagarumin tayi kafin ta iya ɓamɓare Frank daga Brentford.
Rahotanni dai sun bayyan cewa jiga-jigan United sun fi karkata gare shi, amma ganin cewa ba zai zo da arha ba na iya sanyawa su karkata akalarsu zuwa kan wani mai horaswan.
Simone Inzaghi
An daɗe ana danganta kocin Inter Milan Inzaghi da United.
Kociyan ɗan ƙasar Italiya mai shekaru 48, ya lashe gasar Seria A da Inter Milan a kakar wasan data gabata sannan kuma ya lashe Coppa Italia har sau biyu.
Ya kuma kai ƙungiyarsa har matakin wasan ƙarshe na gasar cin kofin zakarun Turai ta 2023 inda ta sha kashi a hannun Manchester City.
Tsohon ɗan wasan Lazio da Italiya ya kuma lashe Coppa Italia a matsayin kocin Lazio, kuma ya shahara wajen samar ingantaccen tsari a ƙungiyoyin da ya jagoranta.
Kwanan nan Inzaghi ya ƙulla sabuwar yarjejeniya da Inter Milan har zuwa 2026.
Kieran McKenna
McKenna koci ne da ya san Old Trafford sosai, inda ya kasance a tawagar masu horasa da Kulob ɗin daga 2016 zuwa 2021.
Ya taka rawar gani a aikinsa na farko a Ipswich Town, inda ya jagorance su daga matakin League One zuwa Firimiya a cikin shekaru biyu da rabi kacal.
Hakan na nufin ba abin mamaki ba ne ana ɗaukar kocin mai shekaru 38 daga Arewacin Ireland a matsayin ɗaya daga cikin manyan masu fatan gudanar da aikin horaswa a Old Trafford.
An alakanta shi da aiki a Brighton da Manchester United da Chelsea a lokacin bazara, bayan da ya kashe fam miliyan 4 kacal a kakar da ta gabata inda ya jagoranci ƙungiyarsa zuwa gasar Premier.
Amma dai, ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekaru huɗu a Ipswich kuma ba ƙaramin kudi United za ta kashe ba idan tana buƙatar ɗaukarsa daga ƙungiyar.
Ruben Amorim
An alaƙanta kocin Sporting, Amorim da Liverpool kafin su naɗa Arne Slot.
Amorim ya jagoranci ƙungiyar Sporting ta lashe kofin gasar Portugal dinta ta farko a cikin shekaru 19 yana da shekaru 36 kacal a shekarar 2021 kuma ya sake lashe gasar karo na biyu da ƙungiyar a kakar wasan da ta gabata.
Tsohon ɗan wasan tsakiya na Benfica da Portugal, Amorim ya yi ritaya a matsayin ɗan wasa a shekara ta 2018 kuma ya fara taka rawar gani a matsayin koci shekara guda bayan nan, inda ya zama kocin ƙungiyar matasa ta Braga.
Ya yi nasara a wasa goma cikin 13 - ciki har da nasarar farko a Benfica na tsawon shekaru 65 - nan da nan ya fara jan hankalin manyan ƙungiyoyi kuma, Sporting ta nuna sha'awar tabbatar da aikinsa inda har ta biya Yuro miliyan 10 don mayar da shi kocinta a watan Maris ɗin 2020.
Amorim dai yana da kwantiragi da Sporting har zuwa watan Yuni, 2026.
Edin Terzic
Edin Terzic ya jagoranci Borussia Dortmund zuwa wasan ƙarshe na gasar zakarun Turai a kakar wasan da ta wuce amma ya bar ƙungiyar a watan Yunin da ta gabata.
Terzic ya fara aikin horaswa ne a makarantar Dortmund tsakanin 2010 zuwa 2013 kafin ya zama mataimakin Slaven Bilic a ƙungiyar Besiktas ta Turkiyya.
Ya bi Bilic zuwa West Ham United a 2015 amma ya bar kulob ɗin na Premier bayan korar ɗan Croatian a watan Nuwamban 2017 kuma ya koma Dortmund a matsayin mataimakin Lucien Favre shekara guda bayan haka.
Bayan korar Favre a watan Disamba 2020, Terzic ya zama kociyan riko har zuwa ƙarshen wannan kakar kuma ya jagoranci ƙungiyar ta lashe gasar cin kofin Jamus inda ta doke RB Leipzig.
Sannan ya yi aiki a matsayin daraktan fasaha na ƙungiyar kafin ya zama kocin ƙungiyar a shekarar 2022.
Xavi
Kofin La Liga guda ɗaya a cikin shekaru biyu da rabi bai isa Barcelona ta ba tsohon ɗan wasan ƙungiyar Xavi damar tsawaita zamansa a mtsayin kocinta ba.
Tsohon ɗan wasan mai shekaru 44, ya yi ƙoƙarin tabbatar da Barcelona cikin jerin manyan ƙungiyoyin duniya duk da take fuskanta na rashin kuɗi, kuma ya shahara wajen samar da salon wasan ƙwallon kafa mai kayatarwa.
Ko a baya bayan nan an yi raɗe-raɗin cewa United ta tattauna da tsohon ɗan wasan tsakiyan kan karɓar ragamar kulob ɗin kuma anan ganin idan har da gaske United ta tuntuɓe shi zai yi wuya ya ƙi komawa Old trafford.
Zinedine Zidane
Zidane dai bai karɓi wani aikii ba tun da ya bar Real Madrid a shekarar 2021.
A baya United ta tuntuɓe shi lokacin da Solskjaer ya tafi a 2021, kamar yadda BBC ta ruwaito a lokacin.
Bafaranshen dai bai taɓa zama koci wajen babban birnin Sifaniya ba, amma rawar da ya taka a Madrid ya sa ya kasance ɗaya daga cikin kociyoyin da ake mutuntawa a duniya.
Ya jagoranci Madrid zuwa lashe gasar zakarun Turai guda uku a jere - inda shi ne kocin da ya taɓa yin haka , kuma ya lashe gasar La Liga a lokacin da ya koma karo na biyu a ƙungiyar. Amma ko wani kulob din da zai iya shawo kan Zidane ya koma aiki bayan Real Madrid?
Da kamar wuya, amma ko shakka samun Zidane a matsayin kocin zai yi matuƙar farantawa magoya bayan United rai.











