Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Plymouth ta yi waje da Liverpool daga FA Cup
Plymouth Argyle, wadda take ta karshe a teburin Championship ta yi waje da Liverpool mai jan ragamar Premier League daga FA Cup na bana.
Koci, Arne Slot ya sauya ƴan wasa 10 a karawar daga waɗanda suka fitar da Tottenham a League Cup, inda suka kai wasan karshe a makon jiya.
To sai dai Plymouth ta yi amfani da damar da ta samu a wasan da ta kai zuwa zagaye na biyar a FA Cup.
Tun farko sun tashi ba ci a zagayen farko, daga nan suka je hutu suka koma fafatawar zagaye na biyu.
An bai wa Plymouth fenariti a minti na takwas da shiga zagaye na biyu, sakamakon da Harvey Elliott ya taɓa ƙwallo da hannu.
Ɗan wasan Plymouth, Ryan Hardie ne ya buga ƙwallon, wanda ya zura a raga da ta kai Liverpool ta kasa farkewa har da ƙarin mintin tara, bayan da lokaci ya cika.
Wannan shi ne karo na huɗu da Liverpool ta yi rashin nasara a dukkan fafatawa a bana, ɗaya a Premier League da a League Cup da Champions League
Pylmouth, wadda take ta karshen teburi, wasa ɗaya ta yi nasara a cikin wata uku baya.
Kocin Plymouth, Miron Muslic yana kokari a ƙungiyar, tun bayan da ya maye gurbin Wayne Rooney.
Liverpool wadda tun farko ke fatan lashe kofi huɗu a bana ta kai wasan karshe a Carabao Cup da za ta yi a watan Maris a Wembley da Newcastle.
Haka kuma ƙungiyar Anfield tana ta ɗaya a kan teburin Premier League da tazarar maki shida da ƙwantan wasa da Everton.
Kuma Liverpool ta kai zagaye na biyu a Champions League, wadda ta ja ragamar teburin sabuwar gasar da aka sauya wa fasali daga kakar nan.