Ƴan wasan Barca da Real da za su kara a wasan ƙarshe na Copa del Rey

Ƴan wasan Barca da Madrid

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

A ranar Asabar ne manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na Sifaniya, Real Madrid da Barcelona za su ɓarje gumi a wasan ƙarshe na gasar Copa del Rey.

Wasan wanda ake yi wa laƙabi da el-classico - na ɗaya daga cikin wasannin da suka fi jan hankalin masoya ƙwallon ƙafa a faɗin duniya.

Ƙungiyoyin sun kawo wannan matakin ne bayan da Real ta doke Real Sociedad da ci 5-4 a wasa gida da waje.

Ita ma Barcelona ta kawo matakin ne bayan fitar da Atletico Madrid da ci 5-4 gida da waje.

Barcelona ce ƙungiyar da ta fi ɗaukar kofin na Copa del Rey a tarihi, bayan da ta ɗauki kofin har sau 31, yayin Real Madrid ta ɗauki kofin sau 20.

A yanzu haka Barcelona ce ta ɗaya a kan teburin La Liga da maki 76, yayin Real Madrid ke matsayi na biyu da maki 72, inda ya rage wasa biyar a ƙarƙare gasar ta bana.

Wasu fitattun ƴan wasan ƙungiyoyin na fama da jinya ciki har da Robert Lewandowski da Eduardo Camavinga, don haka ba za su buga fafatawar ba.

Tuni dai ƙungiyoyin suka fitar da jerin sunayen zaratan ƴan wasan da za su je da su wasan na ƙarshe da za a buga a birnin Seville da ke ƙasar ta Sifaniya.

Tawagar ƴan wasan Real Madrid

Masu tsaron raga

  • Thibaut Courtois
  • Andriy Lunin
  • Fran González

Masu tsaron baya

  • David Alaba
  • Lucas Vázquez
  • Vallejo
  • Fran García
  • Antonio Rüdiger
  • Ferland Mendy
  • Raúl Asencio

Ƴan wasan tsakiya

  • Jude Bellingham
  • Federico Valverde
  • Luka Modrić
  • Aurélien Tchouaméni
  • Arda Güler
  • Dani Ceballos

Ƴan wasan gaba

  • Vinicius Junior
  • Kylian Mbappé
  • Rodrygo
  • Endrick
  • Brahim Díaz

Tawagar ƴan wasan Barcelona

Masu tsaron raga

  • Andre ter Stegen
  • Wojciech Szczęsny
  • Inaki Peña

Masu tsaron baya

  • Pau Cubarsí
  • Ronald Araújo
  • Jules Koundé
  • Iñigo Martínez
  • Andreas Christensen
  • Eric García Martret
  • Héctor Fort
  • Gerard Martín

Ƴan wasan tsakiya

  • Gavi
  • Pedri
  • Dani Olmo
  • Frenkie de Jong
  • Pablo Torre
  • Fermín López

Ƴan wasan gaba

  • Ferran Torres
  • Ansu Fati
  • Raphinha
  • Pau Víctor
  • Lamine Yamal