Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Osimhen ya kammala komawa Galatasaray daga Napoli
Victor Osimhen ya kammala komawa Galatasaray, domin buga mata wasannin aro zuwa karshen kakar bana, kamar yadda ƙungiyoyin biyu suka sanar ranar Laraba.
Galatasaray za ta biya ɗan wasan mai shekara 25 ($6.65 million) a wasannin aron da zai yi mata zuwa karshen yarjejeniyar da za ta kare a karshen watan Yunin 2025.
Osimhen ɗan wasan tawagar Najeriya ya tsawaita kwantiraginsa da Napoli a Disamba, kan zuwa karshen 2026 kan Yuro miliyan 130.
Ƙungiyoyi da yawa sun yi zawarcinsa a bana har da Al-Ahli ta Saudi Arabia, an kuma ce tun farko Chelsea za ta ɗauki ɗan wasan Najeriya.
Osimhen baya cikin ƴan wasa 23 da za su buga wa Napoli Serie A da sauran wasannin bana.
Hakan ya sa ƙungiyar Italiya ta ɗauki ɗan wasan tawagar Belgium, Romelu Lukaku, madadin Osimhen.